Rikici tsakanin jiga-jigan APC ya barke bayan an saka ranar zaben sabbin shugabannin jam'iyya

Rikici tsakanin jiga-jigan APC ya barke bayan an saka ranar zaben sabbin shugabannin jam'iyya

  • Jiga-jigai kuma masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC sun ta martani kan ranar zaben shugabannin jam'iyyar na kasa da aka saka jiya
  • Wani jigo a kudancin kasar nan ya ce idan sun so kada su zabi shugabanni har sai shekarar 2023, ko yaushe aka yi zaben bai dace ba
  • Sai dai, shugaban VON kuma jigon jam'iyyar, ya ce watan Fabrairu ya yi daidai saboda lokacin komai ya natsa kuma za a yi shi hankali kwance

Martani daban-daban sun dinga zuwa bayan an saka watan Fabrairun shekara mai zuwa domin yin zaben sabbin shugabannin jam'iyyar APC da za su yi mulkin shekaru hudu cif.

A watanni 17 da suka gabata, kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar wanda ke karkashin shugabancin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ke jagorancin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Gwamnoni sun bayyana matakin da suka dauka kan kwamitin Mala Buni na APC

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, an kafa kwamitin ne a watan Yunin shekarar da ta gabata sakamakon rikicin da ya barke a cikin kwamitin shugabancin jam'iyyar na Kwamared Adams Oshiomhole.

Rikici tsakanin jiga-jigan APC ya cigaba bayan an saka lokacin taron gangamin jam'iyyar
Rikici tsakanin jiga-jigan APC ya cigaba bayan an saka lokacin taron gangamin jam'iyyar. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Amma kuma, an dinga kiraye-kirayen tsige Buni kan yadda kwamitinsa ke gudanar da al'amuransu.

A ranar Laraban makon da ta gabata, 'yan sanda sun mamaye ofishin jam'iyyar da ke Abuja bayan fusatattun 'yan jam'iyyar sun barke da zanga-zanga kan tsige Buni.

Gwamnan jihar Kebbi kuma sugaban gwamnonin jam'iyyar, Atiku Bagudu ne ya sanar da ranar taron bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Litinin.

Taron ya samu halartar Gwamna Buni da takwaransa na jihar Jigawa, Mohammed Abubakar Badaru.

Bayan taron, Bagudu ya ce an zabi watan ne domin a bai wa jihohi hudu da basu zabi shugabanninsu ba damar yin hakan tare da shagalin Disamba.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Ku jira don jin ta bakinsa a watan Janairu - Fashola game da takarar Tinubu

Hankulan jiga-jigan jam'iyyar ya rabu

Jigo kuma mai fada a ji, tsohon dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar, Chief Chekwas Okorie, ya sanar da Daily Trust cewa, sabon cigaban bai dace a same shi a wannan lokacin ba, ranar da aka tsayar ba ta dace ba.

Hakazalika, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na kudu kudu, Prince Hilliard Eta, ya ce kwamitin bai dace har yanzu ya na mulki ba.

Ya ce, "Idan sun so, su bari sai bayan zaben 2023 su yi zaben, duk da haka basu yin abu yadda shari'a tace."

Amma darakta janar na VON kuma jigon jam'iyyar, Osita Okechukwu, ya ce watan Fabrairun da aka sa ya yi daidai ga jam'iyyar.

Barazanar kora ta daga APC babban abun dariya ne, Sanata Marafa

A wani labari na daban, Sanata Kabiru Garba Marafa ya yi fatali da barazanar da kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC kan korar shi da suke fadin za su yi sakamakon bayyana abinda ke zuciyarsa.

Kara karanta wannan

Kaduna za ta daina dogara da abin da za a samu daga asusun Tarayya - Gwamnatin El-Rufai

Ya kwatanta barazanar da lamarin kawai inda yace jam'iyyar ta koma bin doka ko kuma nan babu dadewa bayanta zai zo, Daily Trust ta wallafa.

Marafa wanda ya taba wakiltar mazabar Zamfara ta tsakiya, a ranar Lahadi ya yi barazanar maka shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar a kotu kan take dokokin da ke kunshe a kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel