Daga Karshe, Gwamnoni sun bayyana matakin da suka dauka kan kwamitin Mala Buni na APC

Daga Karshe, Gwamnoni sun bayyana matakin da suka dauka kan kwamitin Mala Buni na APC

  • Gwamnonin dake karkashin jam'iyyar APC, sun taya gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe murnar karin shekara
  • Gwamnonin sun kuma kaɗa kuri'ar amincewa da kwamitin rikon kwarya na APC, karkashin jagorancin Buni
  • Kwamitin rikon kwarya na Mala Buni na cigaba da fuskantar sabon kalubale daga wasu jiga-jigan APC

Abuja - Gwamnonin jam'iyyar APC sun kaɗa kuri'ar amincewa da kwamitin gwamna Mai Mala Buni, ya cigaba da jan ragamar jam'iyya ta ƙasa.

Jaridar Vanguard ta rahoto gwamnonin sun bayyana cewa kwamitin na rikon kwarya yana tafiyar da jam'iyya ba tare da nuna banbanci ba.

Kwamitin da Buni ke jagoranta, ya tsinci kansa cikin kalubale biyo bayan sukar da yake sha daga fusatattun masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ta APC.

Kara karanta wannan

Kaduna za ta daina dogara da abin da za a samu daga asusun Tarayya - Gwamnatin El-Rufai

Gwamna Buni
Daga Karshe, Gwamnoni sun bayyana matakin da suka dauka kan kwamitin Mala Buni na APC Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A baya-bayan nan, ɗaya daga cikin jigogin APC a jihar Zamfara, Sanata Kabir Marafa, ya kira kwamitin Buni (CECPC) da cewa baya kan doka.

Hakanan kuma, wata kungiyar masu kishin jam'iyyar APC, ta yi kira ga Buni da mambobin kwamitinsa su yi murabus daga aikin su.

Wane mataki gwamnonin APC suka ɗauka?

Sai dai gwamnonin APC, a wata sanarwa da shugabansu, kuma gwamnan Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya fitar, ya taya Buni muranar cika shekara 54, yace yana jan ragamar APC yadda ya dace.

Wani sashin sanarwan yace:

"Muna yaba wa jagorancin da kake yi wajen haɗa kan Najeriya. A matsayin shugaban kwamitin rikon kwarya, muna farin ciki da yadda kake jan ragamar APC ta ƙasa a irin wannan lokaci."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Buhari ya yi magana kan rahoton kisan kiyashin da akai wa masu zanga-zangar EndSARS

"Kazalika mun shaida yadda kake sadaukar da kanka wajen tafiyar da mulkin jihar Yobe, kana kara haskaka gwamnatin APC."
"Yayin da muke taya gwamna Buni Murna, muna cigaba da shirin kawo sabbin shirye-shiryen da zasu samar da aikin yi, habbaka tattalin arziki, da kuma fitar da mutane daga talauci."

Ka shiraya mana taro na ƙasa - Kungiyar APC

Kazalika wata kungiyar masu ruwa da tsaki na APC, ta taya gwamna Buni murnar cika shekaru 54 a duniya, kamae yadda Ripples ta rahoto.

Kuma ta bukaci shugaban kwamitin rikon kwaryan da ya gaggauta fara shirin da ya kamata domin gudanar da babban gangamin jam'iyya na ƙasa.

A wata sanar da ɗaya daga cikinsu, Aliyu Audu, ya fitar, ya yaba wa Buni bisa namijin kokarin da yake duk da kalubalen da ake fama da shi cikin APC.

A wani labarin kuma Jagoran APC Bola Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan mutum 50,000 a wannan jihar da PDP ke jagoranta

Kara karanta wannan

Barazanar sabon yajin aiki: Kakakin Majalisa ya shiga tsakanin ASUU da Gwamnatin tarayya

Shugabannin APC na shirin haɗa wa jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu, mambobin APC 50,000 a jihar Ribas.

A cewar tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Okocha, zasu tabbatar da mara wa Tinubu baya har zuwa ya zama shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel