Da duminsa: Soludo ya magantu kan tsame sunansa daga na 'yan takara a Anambra
- Farfesa Chukwuma Soludo ya ce babu gudu balle ja da baya, yana cikin 'yan takarar kujerar gwamna a Anambra
- Kamar yadda ya sanar, ya ce an yi zaben fidda gwani wanda INEC ta lura da shi kuma shine ya samu nasara a APGA
- Kungiyar da ta fitar da takardar a madadinsa, ta ce tana kira ga magoya bayansu na Anambra da su kwantar da hankalinsu
Chukwuma Soludo, daya daga cikin 'yan takarar zaben gwamnonin da za a yi a jihar Anambra na ranar shida ga watan Nuwamban shekarar nan yace har yanzu yana cikin 'yan takara.
Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta cire sunan shi daga cikin jerin 'yan takara.
KU KARANTA: Mambobin APC sun farfashewa jami'in kotu baki a jihar Ogun
KU KARANTA: 'Yan uwa 3 sun sheka barzahu bayan sun kwashi garar Amala a Ilorin
2023: Yan majalisun Arewa sun bayyana yankin da ya kamata ya fitar da shugaban kasa, sun ambaci zabinsu
A wata takarda da kungiyar yakin neman zabensa ta fitar a madadinsa, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya ce har yanzu shine dan takarar jam'iyyar APGA, Daily Trust ta wallafa.
"Honarabul Chukwuma Umeorji ya bayyana a matsayin dan takarar kujerar gwamna karkashin jam'iyyar APGA a jihar Anambra wanda za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba.
“Wallafar INEC ta yi dogaro ne da wani hukunci na wata babbar kotu dake jihar Jigawa. Ana shawartar miliyoyin magoya bayanmu dake Anambra da sauran sassan duniya da kada su damu da wannan wallafar. Farfesa Chukwuma Charles Soludo zai yi takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APGA.
"An zabe shi tsayawa takara ne dogaro da dokokin zabe da na INEC. INEC ta kula da taron da APGA tayi na ranar Laraba, 23 ga watan Yuni inda ta zabi Soludo wanda ya samu kashi 93.4 na kuri'un da aka kada. An kuma baza taron a gidajen talabijin a kasar nan."
A wani labari na daban, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rangwantawa talakawa. Basaraken yayi wannan kiran bayan karbar bakuncin shugaban kasan a fadarsa a ranar Alhamis.
Ya yi kira ga shugaban kasan da ya inganta tsaro tare da shawo kan matsalar hauhawar farashin kaya a kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.
"Muna godiya ga shugaban kasa kan wannan ziyarar kuma hakan zai kara dankon alakarsa da gidan sarauta. Gidansa ne dama can. Ba za mu iya fadin sau nawa ya zo gidan ba ballantana a zamanin marigayin Sarki, a yayin shagali da babu," yace.
Asali: Legit.ng