2023: Jonathan zai dawo a matsayin shugaban kasa, Shahararren Fasto ya yi hasashe, ya bada sharadin cikar haka

2023: Jonathan zai dawo a matsayin shugaban kasa, Shahararren Fasto ya yi hasashe, ya bada sharadin cikar haka

  • Akwai alamu da yawa da ke nuna cewa Goodluck Ebele Jonathan zai iya shiga takarar shugaban kasa a 2023
  • A takaice dai, hasashen malaman addini a kwanan nan suna ikirarin cewa abubuwan alkhairi da yawa suna jiran tsohon shugaban
  • Daya daga cikin irin wannan ya ce Jonathan zai sake nasara a matsayin shugaban Najeriya a 2023 a jam’iyyar APC

FCT, Abuja - Wani babban fasto na cocin Abuja, The Resurrected Assembly (GROM), Prize F. Aluko, ya yi hasashen cewa Goodluck Ebele Jonathan zai dawo a matsayin shugaban kasa a 2023.

Fasto Aluko a cikin hasashensa na baya-bayan nan ya bayyana cewa Jonathan ya bar ofis a 2015 saboda akwai horo da Allah yake son yi masa kan wasu ayyuka da zai cimma a nan gaba, The Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarki Sanusi ya soki tsarin biyan tallafin fetur, ya fallasa badakalar da ke cikin tsarin

2023: Jonathan zai dawo a matsayin shugaban kasa, Shahararren Fasto ya yi hasashe, ya bada sharadin cikar haka
2023: Jonathan zai dawo a matsayin shugaban kasa, Shahararren Fasto ya yi hasashe, ya bada sharadin cikar haka Hoto: The Sun Nigeria
Asali: UGC

Jagoran na GROM ya kara da cewa yanzu da Allah ya shirya tsohon shugaban kasar, lokaci ya yi da za a bi abin da Madaukakin Sarki ya nufa a kan shi, wanda shine shugabanci.

Sai dai kuma, malamin ya yi gargadin cewa domin Jonathan ya cimma wannan, dole ne ya fice daga Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP ya koma sansanin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Ubangiji ya bayyana cewa an rufe babinsa (Jonathan) a PDP an kuma bude sabon babin tafiyarsa ta siyasa, ba a cikin PDP ba, amma a APC. Cewa dole ya daidaita kansa da manufa da nufin Allah don rayuwarsa ta sami damar cika aikinsa na shugaban ƙasa.
“Allah ya ba shi damar ficewa daga kujerar shugaban kasa da nufin samun damar horar da shi kan abubuwan da yake so ya yi. Yanzu da Allah ya dawo da shi, zai iya cika wannan manufar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke ma'aikacin jinyan MSF da wasu mutum 2 a Zamfara

“Cewa kada Jonathan ya saurari masu jan hankali amma ya fice daga taron su ya bi shawarar Allah. Cewa Allah yana nuna masa yatsa don ya zama Shugaban Najeriya a 2023. Kuma hakan na iya cika ne kawai idan ya yanke shawarar bin nufin Allah ya bar jam’iyyar siyasar da yake a yanzu, ya koma APC.”

A tsaka da rade-radin sauya sheka, tsohon shugaban kasa Jonathan ya gabatar da muhimmiyar bukata gabannin 2023

A gefe guda, tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa da ta ba da damar amfani da na’ura wajen watsa sakamakon kafin 2023.

Premium Times ta ruwaito cewa Jonathan ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba, 29 ga watan Satumba, yayin da yake gabatar da lacca a bikin kaddamar da Kwalejin Tsaron Kasa, a Abuja.

Babban tanadi mai cike da cece-kuce a cikin kudirin shine Sashe na 52, wanda ke magana game da watsa sakamakon zaɓe ta hanyar na’ura.

Kara karanta wannan

‘Yan IPOB sun kashe tsohon Sarki, Mijin tsohuwar Minista da Direban ‘Dan Majalisa a wata daya

Asali: Legit.ng

Online view pixel