Duk da an yi kasafin Naira Tiriliyan 16, ‘Yan Majalisa na so a kara Naira Biliyan 500 a 2022

Duk da an yi kasafin Naira Tiriliyan 16, ‘Yan Majalisa na so a kara Naira Biliyan 500 a 2022

  • Abubakar Kabir yace kudin da za a fitar domin a gina tituna a 2020 ya yi kadan
  • Hon. Kabir ya bayyana cewa ana bukatar a kara wa ma’aikatar akalla N500bn
  • ‘Dan Majalisar yace a halin yanzu ‘yan kwangila na bin Gwamnati Biliyan 650

Abuja - Kwamitin kula ayyuka a majalisar wakilan tarayya tace kudin da aka ware wa ma’aikatar ayyuka da gidaje na kasa a kasafin kudin 2022 ya yi kadan.

Shugaban kwamitin ayyuka na majalisar tarayya, Abubakar Kabir (APC, Kano), ya bayyana wannan. Premium Times ta fitar da rahoto a ranar Alhamis.

Honarabul Abubakar Kabir ya na ganin Naira biliyan 450.02 da aka yi kasafi domin yin ayyuka ba za su isa a gudanar da ayyukan da suka kamata a badi ba.

Kara karanta wannan

Shekara daya da rabi da Shugaba Buhari ya yi magana, har yau umarninsa bai fara aiki ba

Har ila yau shugaba Muhammadu Buhari ya ware wa ma’ikatar Naira biliyan 15.05 domin biyan ma’aikata da wasu Naira biliyan 16.5 na hidima da gudanar wa.

Rahoton yace ‘dan majalisar ya yi wannan jawabi a lokacin da ake tafka muhawara a kan kasafin kudin 2022 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar.

Hon. Kabir yace Naira biliyan 240 za a fitar domin ayyukan tituna duk da cewa ‘yan kwangilar suna bin bashin ma’aikatar tarayyar sama da Naira biliyan 640.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Femi Gbajabiamilla
Shugaban majalisar tarayya, Femi Gbajabiamilla Hoto: von.gov.ng
Asali: UGC

Babu kudin yin ayyuka a shekara mai zuwa?

A cewar Kabir, idan ba a kara kason ma’aikatar ayyuka da gidajen ba, gwamnatin Najeriya ba za ta samu kudin yin ayyuka idan aka cire bashin ‘yan kwangila ba.

“Shugaban majalisa na fahimci wani abu a kasafin ayyuka ta tarayya, kason da aka yi ba zai isa ba. Na lura N280bn kacal aka ware a kasafin kudin 2020.”

Kara karanta wannan

Kasafin kudi: Naira Biliyan 134 sun yi mana kadan inji ‘Yan Majalisar Najeriya

“Kuma akwai takardun ‘yan kwangila suna bin N640bn. Idan aka yi haka, a 2020 ana nufi ba za a samu kudin da za a gina tituna, ayi gadoji ba” – Kabir.

An yi kokari, amma da sauran aiki ...

‘Dan majalisar yake cewa sai an kashe Naira tiriliyan 7 sannan za a iya samar da tituna da ake bukata.

A jawabinsa, Kabir ya yarda gwamnatin tarayya ta kawo tsare-tsaren Sukuk, HDMI, NSIA domin ayi tituna, yace duk da haka ana neman karin Naira biliyan 500.

An ji ‘Dan Majalisar jihar Abia, Benjamin Kalu ya soki abin da aka gutsurawa Majalisar Tarayya daga Tiriliyan 16 da za a kashe a kasafin kudin shekara badi.

Hon. Benjamin Kalu yace ba a kara masu kudi ba duk da an kara Naira Biliyan 200 a kasafin 2022. 'Yan majalisar kasar za su batar da sama Naira biliyan 230.

Asali: Legit.ng

Online view pixel