Kasafin kudi: Naira Biliyan 134 sun yi mana kadan inji ‘Yan Majalisar Najeriya

Kasafin kudi: Naira Biliyan 134 sun yi mana kadan inji ‘Yan Majalisar Najeriya

  • Majalisar Tarayya tace abin da aka ware mata a shekara mai zuwa ya yi kadan
  • Benjamin Kalu yace kason kowa ya karu a shekarar 2022 ban da na majalisar
  • Hon. Kalu ya bayyana haka yayin da ake muhawara a kan kasafin kudin badin

Abuja - A ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba, 2021, majalisar wakilan tarayya ta koka da kudin da aka ware mata a kasafin shekara mai zuwa ya yi kadan.

Da ake tattauna wa a kan kundin kasafin kudin shekarar 2020, Benjamin Kalu wanda shi ne mai magana da yawun ‘yan majalisar wakilai, ya soki kasonsu.

Honarabul Benjamin Kalu yace duk da an kara adadin kudin da ake ba hukumomi da ma’aikatu kai-tsaye, babu canjin da aka samu a kason ‘yan majalisa.

Kara karanta wannan

Duk da an yi kasafin Naira Tiriliyan 16, ‘Yan Majalisa na so a kara Naira Biliyan 500 a 2022

Kalu mai wakiltar mazabar Bende a jihar Abia a majalisar wakilan tarayya yace kason majalisar tarayya bai canza daga abin da aka ba su a shekarar nan ba.

Muhawara a kan kasafin kudin 2022

“Wannan ya shafi majalisa saboda an kara kason wadanda ake tura wa kudi kai-tsaye, an samu kari daga N484bn zuwa N768.2bn.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wannan ya nuna karin 58.7%; karin kusan N283.79bn. Kun san cewa wannan kari bai shafi abin da ya shigo majalisar tarayya.” – Kalu.

Majalisar Najeriya
Majalisar Wakilan Tarayya Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Mai magana da madadin ‘yan majalisar tarayyar kasar ya koka da cewa akwai lokacin da gwamnatin tarayya ta rage kasafin kudin da aka gabatar mata.

Sai kuma aa gaa wannan shekarar babu ko sisi da aka kara a abin da ake ba masu yin dokokin.

‘Amma ku tuna, lokacin da muka nemi mu kashe Naira biliyan 150, sai aka rage kason zuwan Naira biliyan 128”

Kara karanta wannan

Dan majalisa ga FG: Makuden kudi kafintoci da direbobi ke samu, a wajabta musu haraji

“Muna fama da kalubalen kudin canji, da kuma rashin kudin-shiga. Meyasa har yanzu muke a kan Naira biliyan 134?”
“Kun san duka-duka nawa ne Naira biliyan 134 a kason kudin da za a tura kai-tsaye.” – Kalu.

Sanatoci da 'Yan Majalisa za su ci N200bn

Dazu kun ji cewa Sanatoci da 'Yan Majalisa za su ci Naira biliyan 234 a shekarar badi. Kuma Babu wanda ya san abin da kasafin kudin 'Yan Majalisar kasar ya kunsa.

Akwai Naira Biliyan 100 da ‘Yan Majalisar Tarayyar za su kashe wajen kwangiloli. Ragowar kudin za su tafi ne wajen biyan makudan albashi, alawus da gudanar wa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel