Wurare 6 Garanti Da 'Yan Mata Za Su Samu Mazan Aure Da Suka Dade Suna Mafarki

Wurare 6 Garanti Da 'Yan Mata Za Su Samu Mazan Aure Da Suka Dade Suna Mafarki

  • Rayuwa ta sauya musamman yadda samun mijin kwarai ko mata ta gari ke kara wahala
  • Mafi yawancin 'yan mata na tunanin yadda za su samu irin kalan mijin da suke so
  • Hakan bai rasa nasaba da cewa mafi yawan lokuta maza ne ke tunkarar mata a soyayya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Duk da cewa ana iya samun miji ko mata a ko ina kuma a kowane lokaci, amma akwai wurare da dama da suka fi dacewa da kuma saukin samun abokin zama.

Mafi yawan 'yan mata na tambayar kansu, a ina zan samu miji na gari wanda yake da dukkan abubuwan da nake bukata.?

Wurare 6 Da 'Yan Mata Za Su Samu Samarin Aure Da Suka Dade Suna Mafarki
Wuraren Da 'Yan Mata Za Su Samu Mazajen Aure Da Suke Muradi. Stock Photo, GettyImages.
Asali: Getty Images

Akwai mazaje a layi da ba su da budurwa wadanda suke neman aure ido a rufe, samun irinsu yafi komai sauki.

Ba tare da ba ta lokaci ba, wadannan su ne wuraren da za ki samu miji na gari a cikin sauki, kamar yadda TheCable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Hanyoyi 4 na kare kai daga fadawa ta'addanci bayan cire tallafin man fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Wurin bukukuwan daurin Aure

Idan kina son samun miji cikin sauki dole ki kasance kina halartar wuraren taruwar jama'a musamman wurin daurin aure.

Wuraren daurin aure na samun halartar mutane daban-daban da mafi yawanci ba su da aure.

Amfanin neman saurayi a wurin daurin aure shi ne samun shi ba zai yi wahala ba saboda dole za a samu wanda ko wadanda suka san shi a wurin.

Shawara ga 'yan mata, duk lokacin da aka gayyace ki bikin aure, ki yi gaggawar zuwa saboda baki san me zai faru gobe ba.

2. Taron karawa juna sani ko horo

Irin wadannan tarurruka na da muhimmanci wurin samun mijin aure mai irin tunanin budurwa, a nan ne za ki samu miji sai tunanin ci gaba da kuma hangen nesa.

Saboda yanayin taron da kika halarta, kina iya samun irin kalan mijin da ki ka dade kina hankoro a rayuwarki.

Kara karanta wannan

Dalilai 6 Da Suka Janyo Rage Yawan Amfani Da Man Fetur A Mulkin Tinubu

3. Wuraren tarurrukan addini

Idan mace ta kasance mai son addini, irin wadannan tarurruka su ne wuraren da suka fi dacewa da samun miji na gari kuma mai tsoron Allah, cewar Premium Times.

Babbar alama ta samun miji na gari shi ne ya kasance ya na son addininsa da kuma halartar wuraren addini.

4. Wuraren motsa jiki

A irin wadannan wurare, mata da yawa sun samu mazajen da suke mafarkin kasancewa da su.

Mazaje da dama na halartar wuraren motsa jiki don inganta lafiyarsu da kuma samun nitsuwa.

Wannan wuri ne da za ki yi amfani da shi wurin fara wata mu'amala ta soyayya da wani wanda ya kwanta miki a rai.

Akwai hanyoyi da dama da za ki fara magana da wani a wurin, misali ki nemi taimako a wurin shi na koya miki yadda ake amfani da wani injin motsa jiki a wurin, daga nan komai na iya faruwa.

Kara karanta wannan

“Mafita Ga Tsadar Fetur”: Bidiyon Matashi Yana Tuka Babur Mai Cin Mutum 7 Da Ke Aiki Da Lantarki Ya Yadu, Ya Burge Yan Najeriya

Wasu matan na son maza wadanda ke gina jikinsu ta hanyar motsa jiki, idan kina daya daga cikinsu, kakarki ta yanke saka.

5. Taron kungiyoyin ayyukan sa kai

Mafi yawan mutane yanzu ba su fiye yin ayyukan sa kai da taimakon jama'a ba, ba tare da samun ko kwabo ba, cewar My Dating Hacks.

Alamun miji na gari shi ne wanda ya sadaukar da kansa don ya taimaki mutane ba tare da an biya shi wasu kudade ba.

Saboda haka, shiga irin wadannan ayyuka zai taimaka miki wurin samun mijin da ya dace da ke.

6. Wuraren wasanni da bukukuwa

Mafi yawan maza na sha'awar harkokin wasanni da suka hada da kwallon kafa da kwallon kwando da sauransu.

Yayin da mata kuma a bangaren su ba su cika damuwa da wasanni ba.

Zuwanki irin wadannan wurare zai jawo hankalin mazaje zuwa gare ki saboda babu 'yan mata a wurin sosai, daga nan komai na iya kasancewa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Ƙara Samun Fashewa a Najeriya, Mutane Sama da 20 Sun Mutu

Duk da cewa wadannan wuraren da aka lissafo na iya baki daman samun mijin aure, kada ki manta kaddara na iya faruwa ta kowane hali.

Soyayya na iya afkuwa ta inda dan Adam bai yi tsammani ba.

Budurwa Ta Yi Alkawarin Ba Wa Duk Namijin Da Ya Aureta Gida, Mota Ma Miliyan 50

A wani labarin, wata budurwa ta yi alkawarin ba wa duk namijin da ke son aurenta makudan kudade.

Budurwar ta yi alkawarin ba da kyautar gida da mota da kuma miliyan 50 ga duk wanda ya yi nasarar aurenta.

Ta ce tuni mutane da dama suka fara kwankwasa mata kofa, amma ta ce da sharadin ba zai mata kishiya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel