Zan Ba Duk Namijin Da Ya Aureni Gida, Mota Ma Miliyan 50 Amma Da Sharadin Ba Kishiya, Matashiyar Budurwa

Zan Ba Duk Namijin Da Ya Aureni Gida, Mota Ma Miliyan 50 Amma Da Sharadin Ba Kishiya, Matashiyar Budurwa

  • Wata matashiyar budurwa ta nuna muradinta na son shiga daga ciki sannan ta sanya garabasa a kai don jan hankalin yan maza
  • Matashiyar ta yi alkwarin ba duk namijin da ya yi nasarar mallakarta gida mota, da kudi naira miliyan 20
  • Budurwar wacce ta ce tuni aka fara aika mata da sakonni ta ce sharadin auren shine ba za a yi mata kishiya ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata kyakkyawar budurwa yar arewa ta nuna aniyarta na son shiga daga ciki inda ta fito dandalin soshiyal midiya domin tallata kanta.

Domin karfafawa maza gwiwar neman aurenta, matashiyar ta yi alkawarin baiwa duk wanda ya yi nasarar samunta gida, mota da kuma kudi har naira miliyan 50.

Matashiyar budurwa na neman mijin aure amma bata son kishiya
Zan Ba Duk Namijin Da Ya Aureni Gida, Mota Ma Miliyan 50 Amma Da Sharadin Ba Kishiya, Matashiyar Budurwa Hoto: @northern_blog
Asali: Twitter

Duk wanda ya yi nasarar aurena ba zai yi mun kishiya ba, budurwa

Sai dai kuma ta gindaya sharadi guda cewa duk namijin da ya aureta ba zai yi mata kishiya ba.

Kara karanta wannan

“Wa Ya Shirya Aurena”: Baturiya Ta Yi Alkawarin Bayar Da Kyautar Biza Ga Duk Mutumin Da Ya Shirya Aurenta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, a wata hira da aka yi da matashiyar domin tabbatar da ko da gaske take, ta jadadda maganar tata, inda ta ce tuni maza suka fara aiko da sakonni domin shiga sahun manemanta.

Ta kuma bayyana cewa zuwa nan da yan kwanaki za a gama tantance su sannan za a sanar da wanda ya yi nasara da zaran an kammala.

Kalli bidiyonta a kasa:

Jama'a sun yi martani

@HaleematourS ta yi martani:

"@kabirusaje @Nur_al_qalb Ga bahillata bari na ajiye lambobinku kila cikin ku wani ya dace…"

@kabirusaje ya ce:

"Hahahaha wanan ai Koila ce yanzu take tasawa mun barwa kanurai #kanuri saboda sunason auren fararen fulani."

@SirKuliKuliZaid ya ce:

"Gaskiya wannan Bata da Miliyan biyar ma, balle 50 da gida da mota. Duk mayen da yaje yakai kansa."

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Maimaita Tufafin Da Mataifiyarta Ta Sanya Shekaru 29 Da Suka Gabata a Ranar Aurenta

@majidadii__ ya ce:

"Ji kanta kama miliyan 50."

@Y_Lingz:

"Dan Allah Ayi man Hanya Ta Ita Mana Nima Nashiga Cikin Yan Takara Mana 07061551336."

@mal_bukar:

"Daga karshe wannan shiri kamfanin amsaco ne ya daukii nauyin kawo maku."

@hetchkhaby:

"Ko da Baba Buhari za a nunosu tare a NTA yana ɗaga hannunta to bazan shiga wannan gasar ba."

@Mubato_nigeria:

"A ina ake shiga gasar toh?"

Matashiya ta shiga rudani bayan mai gidansu ya nemi soyayya da ita

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa ta shiga tsaka mai wuya bayan mai gidansu ya gabatar mata da wata bukata mai ban mamaki.

A cikin wata wallafa da ta yi a shafinta, ta bayyana cewa mai gidansu ya nemi su yi ban gishiri na baki manda a tsakaninsu wato ya nemi su kulla alaka sai ya yafe mata kudin haya idan ta yarda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel