Dalilai 6 Da Suka Haddasa Rage Yawan Amfani Da Man Fetur A Mulkin Tinubu

Dalilai 6 Da Suka Haddasa Rage Yawan Amfani Da Man Fetur A Mulkin Tinubu

  • 'Yan Najeriya na cikin wani irin mawuyacin halin tun bayan cire tallafin mai da Shugaba Tinubu ya yi
  • Dalilin haka, Gwamnatin Tarayya ta koka kan yadda amfani da man fetur ya ragu a kasar sosai
  • Legit.ng Hausa ta jero muku dalilan da suka sa jawo amfani da man a fetur ya ragu sosai a kasar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - A kwanakin nan hukumar kula da albarkatun mai ta Najeriya ta koka kan yadda amfani da man ya ragu a kasar.

Hukumar ta ce amfani da man fetur din ya ragu da fiye da kashi 28 a watan Yuni kadai na wannan shekara.

Dalilai 6 Da Suka Haddasa Rage Yawan Amfani Da Man Fetur A Mulkin Tinubu
Tun Bayan Cire Tallafin Man Fetur Aka Rage Yawan Amfani Da Man Fetur A Najeriya. Hoto: Nairametrics.
Asali: UGC

Amfani da man fetur din a wurin 'yan kasar ya ragu sosai a watan Yuni daga lita miliyan 66.9 zuwa lita miliyan 40.43 a rana.

Kara karanta wannan

“Mafita Ga Tsadar Fetur”: Bidiyon Matashi Yana Tuka Babur Mai Cin Mutum 7 Da Ke Aiki Da Lantarki Ya Yadu, Ya Burge Yan Najeriya

Akwai wasu dalilai da dama da suka sa amfani da man fetur din ya ragu a kasar ganin yadda man ya yi tsada yadda mutane ba sa iya amfani da shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng ta tattaro muku dalilan da suka jawo yawan amfani da mai din ya ragu a kasar.

1. Cire tallafin mai

Cire tallafin mai da Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi a ranar 29 ga watan Mayu na daga cikin babban dalili.

Cire tallafin ya jawo tsadar man fetur wanda mutane da dama suka rage siya saboda tashin farashin litar.

2. Samar da wata hanya ba fetur ba

Mutane sun gwammace samun wata hanya da za su ci gaba da gudanar da rayuwarsu ba tare da man fetur ba.

'Yan Najeriya da dama sun koma amfani wuta mai hasken rana ta 'Solar' a shaguna da kuma gidajensu.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Ƙara Samun Fashewa a Najeriya, Mutane Sama da 20 Sun Mutu

Sannan yin amfani da Gas a mafi yawan abubuwan da ake amfani da su shi ma na daga cikin dalilan.

3. Wadatar wutar lantarki

A kwanakin nan mutane suna samun wutar lantarki a wadace sabanin yadda ake ba da ita a baya.

Hakan ya sa an rage yawan amfani da man fetur don zuba wa a injunan samar da wuta don gidaje ko kuma a wuraren kasuwanci.

4. Tsadar kayayyaki

Tashin farashin kayayyaki a kasar na daga cikin dalilan da suka jawo rage amfani da fetur saboda matsin tattalin arziki.

Dalilin haka, 'yan Najeriya sun zabi rage amfani da fetur da kuma tafiye-tafiye musamman wadanda ba su zama dole ba saboda yanayin tattalin arzikin kasar.

5. Amfani da fetur din yadda ya dace

Mutane da dama sun yi hankali wurin amfani da man fetur tun bayan da litar mai ta kara tsada.

An yi ta wayarwa mutane kai akan hanyoyin da za su rage almubazzaranci wurin amfani da man fetur din.

Kara karanta wannan

Yadda Marigayi Albani Ya Hango Janye Tallafin Man Fetur Shekaru 9 da Suka Wuce

Hakan ya yi tasiri wurin rage yawan amfani da man a kasar.

6. Sauya gudanar da rayuwa

Mutane da dama yanzu sun dauki matakin sauya rayuwarsu dai-dai da abin da suke samu.

Abin mamaki, za ka ga mutane na tafiya da kekuna ko da kafa musamman wuraren ba su zama dole zuwa da abin hawa ba.

Wannan dalili ya taimaka sosai wurin rage yawan amfani da man fetur a kasar.

Rashin Ciniki Da Tarun Matsalolin Da Masu Gidajen Mai Ke Fama Da Su Bayan Cire Tallafi

A wani labarin, tun bayan cire tallafi a Najeriya, mutane suke cikin wani hali na tsadar man fetur a kasar.

Mutane na kokawa kan yadda Shugaba Tinubu ya cire tallafin ba tare daukar wani matakin kiyaye tsadar mai ba.

Masu gidajen mai suma sun ce fa ba iya mutane ne kawai ke fama da matsalar ba, su ma harkar kasuwarsu na daf da rugujewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel