Basaraken da Ake Ji da Shi a Najeriya, Ya Zama ‘Dan Fim, Ya Fito a Wasan Kwaikwayo

Basaraken da Ake Ji da Shi a Najeriya, Ya Zama ‘Dan Fim, Ya Fito a Wasan Kwaikwayo

  • Sarkin Ife, Adeyeye Enitan Ogunwusi ya na cikin wadanda suka fito a wasan fim na ‘Take me home’
  • Mai martaba ya nuna al’ada da sarautar kasar Yarbawa a wannan wasa da aka shirya a Hollywood
  • Wannan ne karon farko da babban Basaraken mai shekaru kusan 50 zai bayyana a wasan kwaikwayo

Osun - Mai martaba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya fito a wani shirin wasan kwaikwayo, wanda shi ne karon farko da Sarkin Ife ya shiga fim.

Jaridar Aminiya ta kawo rahoto a karshen makon nan cewa Sarkin Ife yana cikin taurarin fim dinnan na ‘Take Me Home’ da aka shirya a Hollywood.

A wannan fim da aka yi a kasar Amurka, Sarkin Ife,Adeyeye Enitan Ogunwusi ya fito a matsayin da ya dace da shi na babban Basaraken kasar Yarbawa.

Kara karanta wannan

Manya basu tsira ba: 'Yan bindiga sun tare motar kwamishinar mata, sun yi awon gaba da ita

An shirya wannan fim ne a birnin Kalifoniya a kasar Amurka a karkashin masana’antar Hollywood da aka kafa shekaru fiye da 110 da suka wuce.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, fitowar mai martaba a wannan fim zai karawa masana’antar Amurkan kima, daraja da martaba a idon Duniya.

Wasan 'Take me Home'

Jaridar nan ta Premium Times ta ce wannan wasan kwaikwayo na ‘Take me Home’, ya nuna irin tasirin al’adar Yarbawa a kasashen yammacin Duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Basarake
Sarakuna a Fadar Aso Rock Villa Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

A shirin, an yi yunkurin nuna al’adar mutanen Afrika da irin jajircewa da yarda da kansu.

Abin da ya faru a fim din shi ne wasu mutanen kasar Amurka sun samu kan su a wani irin hali bayan diyarsu ta sanya rigar mutanen Ile-Ife da aka sato.

Wannan lamari ya jefa iyayenta da daukacin dangin Amurkawa a cikin matsala musamman bayan alkawarin da wasu mutanen Afrika suka yi masu.

Kara karanta wannan

Assha: Na Kusa Da Buhari Sun Fi Damuwa Da Batun Sauyin Kudi, Minista Ya Bayyana Gaskiyar Abin da Ke Ransa

Yadda aka shirya wasan

Dotun Taylor wanda masanin tarihi da al’adu ne ya shirya wannan fim mai dauke da ban dariya da abin tsoro wanda zai kayatar da farare da bakaken fata.

A fim din akwai taurari irinsu, Dave Sheridan, Amber Rivette, Felissa Rose, da Meji Black. Akwai su Abdullateef Adedimeji da Bayo Bankole (Boy Alinco).

Cire mutanen Sanusi a CBN

A wani rahoto, kun ji an tona yadda Godwin Emefele ya kori na-kusa da Muhammadu Sanusi a lokacin da ya zama Gwamnan babban banki.

Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ya ce Emefele yana shiga ofis, ya tsige shi domin a ba Surukinsa mukamin Shugaban NSPM ba tare da ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel