Yadda Godwin Emefele ya kori na-kusa da Sanusi a CBN, ya ba Surukinsa mukami

Yadda Godwin Emefele ya kori na-kusa da Sanusi a CBN, ya ba Surukinsa mukami

  • Sarki Ahmad Nuhu Bamalli ya bada labarin haduwarsu da Godwin Emefiele da ya zama Gwamnan CBN
  • A lokacin da Godwin Emefiele ya canji Sanusi Lamido, ya cire duk manyan mutanen da suka yi aiki da shi
  • Wannan ya jawo aka yi wa Ahmad Nuhu Bamalli da wasu Darektocin NSPM ritaya da karfi da yaji a 2014

Kaduna - Mai martaba Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ya bada labarin wani abu da ya faru a bankin CBN, wanda da yawa ba su san da batun ba.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin Albaniy TV, Sarkin ya fadi yadda Godwin Emefiele ya sauke su daga Kamfanin buga kudaden Najeriya watau 'National Printing and Minting' jim kadan bayan an nada shi.

Kara karanta wannan

Ministan Jonathan Ya Fadawa Kotu Yadda Aka Wawuri Kudin B/Haram Domin Ayi Kamfe

Tsakanin 2011 zuwa 2012 aka samu matsala a kamfanin NSPM da ke da alhakin buga kudi a Najeriya, hakan ya jawo tafiyar Emmanuel Ehidiamhen Okoyomon.

Mai martaban ya ce dakatar da Emmanuel Ehidiamhen Okoyomon ya yi sanadiyyar da shi ya zama shugaban rikon kwarya a kamfanin na watanni har 21.

Sanusi ya tafi, an kawo wani

Ana haka ne sai sabani ya shiga tsakanin Gwamnan CBN, Sanusi Lamido Sanusi da shugaban kasa na wancan lokaci watau Dr. Goodluck Ebele Jonathan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bidiyon, za a ji Mai martaba yana cewa bayan Goodluck Jonathan ya nada Godwin Emefiele a CBN, sai sabon Gwamnan ya nuna ba zai yi aiki da su ba.

Sanusi II
Sanusi II tare da Sarkin Zazzau Hoto: hutudole.com
Asali: UGC

Emefiele ya ki yarda ya tafi da duk wasu wadanda aka nada a ofis a lokacin Sanusi yana babban banki, a dalilin wannan aka yi wa mutum uku ritaya.

Kara karanta wannan

Sabon Tsari: CBN Ya Ƙara Shigo da Abu 2 da Zasu Rage Wa 'Yan Arewa Wahalar Neman Sabbin Kuɗi

Ahmad Nuhu Bamalli sun tafi...

"Bayan an nada shi, ranar da ya fara zuwa taron shugabanni bayan watanni shida, na fara karanto takardu sai ya kalle ni, ya ce yana so ya kawo mutanen shi
Bai so ya yi aiki da mu Darektoci da muka yi aiki da Sanusi Lamido Sanusi, ya yi mana ritaya amma ba mun yi laifi ne ba, muka yi ritaya da karfi da yaji kurum."

- Ahmad Nuhu Bamalli

Mai martaban ya ce washegari aka biya su duka hakkokinsu, aka nada sababbin shugabanni.

Legit.ng Hausa ta binciki lamarin, ta tabbatar da a Satumban 2014 aka cire Darektocin kamfanin buga kudin, aka kawo Joseph Ugbo da Abbas Masanawa.

...An kakaba Joseph Ugbo

Sarkin Zazzau ya cenan take Gwamnan CBN ya yi hanyar da Joseph Ugbo wanda surukinsa ne ya zama cikakken shugaba ba tare da bin ka’idojin aiki ba.

Shi Ugbo ya yi aiki ne kamfanoni irinsu Unilever da Dangote Flours a Kalaba, ya yi karatu a Legas, ya maye gurbin Bamalli wanda daga baya ya zama Sarki.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Yiwa Tsohon Sarkin Kano Sanusi Wankin Babban Bargo

Bashin Najeriya ya taru

Rahoto ya zo cewa zuwa karshen Satumban shekarar bara, gwamnatin tarayya ta karbo aron Naira Tiriliyan 42, bashin kasar ya karu da 2.85% a watanni uku.

Yawan karbo bashi da ake yi ya jawo Muhammadu Buhari zai bar mulki ana bin duk ‘Dan Najeriya N220,000 idan da a ce za a rabawa mutanen kasar nan bashin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel