Assha: Ministan Buhari Ya Daga Murya, Ya Ce Karancin Naira Na Jefa 'Yan Najeriya a Kunci

Assha: Ministan Buhari Ya Daga Murya, Ya Ce Karancin Naira Na Jefa 'Yan Najeriya a Kunci

  • Babatunde Fashola ya bukaci babban bankin Najeriya (CBN) ya sake nazari kan manufarsa na sauya kudi
  • Ministan ayyuka da gidaje ya ce wannan manufa na CBN na kuntatawa al'ummar Najeriya sosai
  • A cewar Fashola shine dalilin da yasa Bola Tinubu ya fito ya yi magana ba wai don son zuciyarsa bane

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya ce manufar sauya naira da babban bankin Najeriya (CBN) ya yi yana kuntatawa yan Najeriya kuma akwai bukatar sake duba shi, TheCable ta rahoto.

Babban bankin ya sanya ranar 10 ga watan Fabrairu a matsayin sabon wa'adin daina amfani da tsoffin kudi a kasar.

Fashola
Assha: Ministan Buhari Ya Daga Murya, Ya Ce Karancin Naira Na Jefa 'Yan Najeriya a Kunci Hoto: TheCable
Asali: UGC

Da farko CBN ya saka ranar 31 ga watan Janairu a matsayin wa'adin ne amma sai ya zamana yan Najeriya da dama sun gaza samun sabbin takardun kudin na N200, N500 da N1000, lamarin da ya haddasa karancin kudi a kasar.

Kara karanta wannan

Sabon Tsari: CBN Ya Ƙara Shigo da Abu 2 da Zasu Rage Wa 'Yan Arewa Wahalar Neman Sabbin Kuɗi

Da yake zantawa da Morayo Afolabi-Brown, mai gabatar da shirye-shirye a ranar Laraba a wani shirin kai tsaye ta Instagram, Fashola ya ce dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, yana yiwa yan Najeriya yaki ne lokacin da ya nuna damuwarsa kan karancin sabbin kudin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fashola ya ce:

"Ina tausayawa mutanen Najeriya da yanayin da suka shiga. Wasu lokutan manufofi suna zuwa haka idan ana cikin aiwatar da su, wasu lokutan zai tafi daidai sannan wasu lokutan sai an sake duba su tare da dake nazari a kansu.
"Duk da cewar CBN ya yi aiki ne bisa tafarkin yancin da doka ya bashi, yana da matukar muhimanci mu tuna cewa al'umma muke yi wa aiki kuma al'umman sun ce yana sa su kunci, yana da muhimmanci a dan ja baya sannan a tambaya a ina ne ake kuntata masu da kuma yadda za mu iya inganta shi. Ba lallai ne ya zama batun son kai ba.

Kara karanta wannan

Wahalar Naira Da Mai: Akwai Wasu Na Kusa Da Buhari Da Basu Son Tinubu Yaci Zabe, El-Rufa'i

"Ya zama dole a jinjinawa dan takararmu kasance shi daya daga cikin mutanen farko, mutum na farko da ya fara magana cikin yan takarar a Abeokuta.
"Koda dai wasu sun gaggauta cewar yana yakar Buhari ne ko yana yiwa jam'iyyarsa yaki ne amma yanayinsa ne haka a matsayinsa na mai yiwa jama'a yaki. Dan takararmu bai ce kada a chaja kudi ba amma hakan yana kuntatawa mutane.
"Saboda haka akwai bukatar a sake duba batun aiwatar da shi."

Ba Tinubu ke juya ni ba, Fashola

Ministan ya kuma bayyana cewa shi ba dan abi yarima a sha Tinubu bane a lokacin da yake gwamnan jihar Lagas amma ya kan tuntube shi kan lamura saboda gogewarsa.

Ku fara biyan sabbin kudi a kanta, CBN ga bankuna

A halin da ake ciki, babban bankin CBN ya umurci bankunan Najeriya da su fara biyan kwastamomi sabbin kudi a kan kanta.

Gwamnan bankin, Godwin Emefiele ne ya bayar da wannan umurnin don ragewa jama'a radadin da suke ciki a yanzu da kuma rage cunkoso a ATM.

Asali: Legit.ng

Online view pixel