Dan Mai Karfi: Bakanike Mai Daukar Injin Mota Shi Kadai Ya Bayyana a Bidiyo

Dan Mai Karfi: Bakanike Mai Daukar Injin Mota Shi Kadai Ya Bayyana a Bidiyo

  • Wani bakanike ya baiwa mutane mamakin karfinsa bayan ya iya daukar injin mota da hannunsa shi kadai
  • Ba tare da sa masa hannu ba, mai karfin ya 'dane kan motar kuma ya daga injin sama lokaci guda
  • Bidiyon wanda aka daura a shafin Instagram ya tayar da kura inda wasu suka ke jinjina masa

Wani bakanike mai karfin gaske ya bada mamaki a garejin kanikawa inda ya nuna bajintarsa wajen daga Injin mota mai nauyin gaske.

A bidiyon da ya yadu a shafin Instagram, bakaniken shi kadai ya daga injin sama kuma ya fitar ba tare da taimakon wani ba.

Yayinda ya fita da Injin daga cikin motar, ya daura a kirjinsa kuma yayi gaba da ita tamkar abu mara nauyi.

Engine Mechanic
Dan Mai Karfi: Bakanike Mai Daukar Injin Mota Shi Kadai Ya Bayyana a Bidiyo Hoto: @gossipmill
Asali: Instagram

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Kera Motar Wasan Tsere Da Hannunsa, Ya Tuka Ta a Hanyar Edo, Bidiyon Ya Yadu

Ya bada mamaki

Wannan bajinta da mutumin ya nuna ya baiwa ma'abota Instagram mamaki inda suka jinjina masa.

Yayinda wasu ke kiransa da 'Mai Karfi' wasu na cewa dan wahala ne, akwai wasu hanyoyin daga injin cikin sauki.

A cewar Mechanic Base, nauyin injin mota na farawa ne daga kilo 140 zuwa 320.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a kan bidiyon:

@karobenedict yace:

"Wani ai karamin abu ne."

@nolimitflyy yace:

"Wajibi namiji yayi gwagwarmaya amma cutar Hernia fa na nan.!."

@donjay840 yace:

"Ku zabi mutanen kwarai..irin wadannan mutane masu kokari ne suka fi karancin albashi a kasar nan kuma ba haka ya kamata ba. Ina jinjinawa dukkan mazajen fama da mata."

@dannyoleg60 yace:

"Lokacin tsufa zai gaya musu."

@daddy_mastiff yace:

"Wannan ba nuna karfi bane. Kawai yana batawa wani mota ne."

Dan Najeriya ya kera sabuwar mota Benz

A wani labarin kuwa, Legit.ng ta ruwaito labarin wani dan Najeriya da ya gina karamar mota kirar Mercedez Benz irin na wasan yara.

Kara karanta wannan

Bidiyon Zabgegiyar Damisa Tana Takun Isa Cikin Jama'a Da ke Shakatawa ya Janyo Cece-kuce

Yaron, wanda aka ce dan asalin jihar Abiya ne ya baja kolin motar a bainar jama'a.

Mutane sun taru a wajen da yake wasa da mota kuma suna tofa albarkatun bakinsu kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel