Gwamna Ya ba da Mamaki da Ya Fadi Kudin da ake Biyan Shi duk Wata
- Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, ya bayyana cewa albashinsa na wata-wata ya kai N503,000, yayin da manyan sakatarorin gwamnati ke karɓar N900,000
- Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta ƙara wa manyan sakatarori albashi ne bayan sun koka cewa daraktoci suna karɓar kusan albashi iri ɗaya da nasu
- Oborevwori ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin ƙaddamar da gidaje guda 12 da motoci 12 ga sababbin sakatarorin a Asaba, babban birnin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Asaba – Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya bayyana adadin albashin da yake karɓa a matsayin gwamnan jihar, yana mai cewa N503,000 ne a wata.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa manyan sakatarorin gwamnati na jihar suna karɓar N900,000 a wata, yayin da Shugaban Ma'aikatan Gwamnati ke karɓar Naira miliyan 1.

Kara karanta wannan
Yadda dalibin tsangaya ya tsallake rijiya da baya lokacin da abokansa 4 suka rasu a Kano

Source: Facebook
Punch ta ruwaito cewa Oborevwori ya bayyana hakan ne yayin bikin ƙaddamar da gidajen bene guda 12 masu ɗakuna huɗu ga sakatarorin da kuma rabon motocin aiki guda 12 ga sababbin waɗanda aka naɗa.
Albashin gwamnan Delta
Oborevwori ya ce gwamnatin jihar ta ƙara wa sakatarorin albashi ne bayan sun nuna cewa daraktoci da dama suna karɓar kusan irin albashin da suke samu.
The Sun ta rahoto ya ce:
“Lokacin da sakatarorin suka ce yawancin daraktoci suna karɓar kusan irin abin da suke samu, sai muka ƙara musu kuɗi. Yanzu manyan sakatarorin gwamnati, albashinku N900,000 ne, nawa kuma N503,000 ne, albashin gwamna.”
Gwamnan ya ƙara da cewa Shugaban Ma'aikatan Gwamnati yana karɓar N1m a wata, yana mai cewa wasu daga cikin ma'aikatan ba sa son mazajensu su san adadin kuɗin da suke karɓa.
Batun tallafa wa ma'aikata
Oborevwori ya ce gwamnatinsa ta sanya jin daɗin ma'aikatan gwamnati cikin abubuwan da take bai wa muhimmanci tun bayan hawanta mulki.

Kara karanta wannan
FAAC ta cika aljihun gwamnatin Tinubu da jihohi, an raba abin da ba a taba samu ba
Ya ce gwamnatin ta samar da motocin aiki ga sakatarorin gwamnati domin ƙara musu sauƙin gudanar da ayyukansu da kuma inganta ayyukan gwamnati.
“Domin inganta zirga-zirgarsu da ayyukan da suke gudanarwa, mun samar da motocin aiki ga manyan sakatarorin gwamnati. A yau kuma ina farin cikin gabatar da wasu motoci 12 ga sakatarorin da aka naɗa kwanan nan,”
In ji shi.
Gwamnan ya bayyana cewa ma'aikatan gwamnati 302 sun amfana da shirin lamunin sayen motoci na jami'an gwamnati, yayin da wasu 119 suka amfana da shirin lamunin gidaje.

Source: Facebook
Ya kuma ce gwamnatin ta samar da kayan noma ga ma'aikatan da ke son shiga harkar noma domin samun ƙarin hanyar samun kuɗi da kuma taimakawa wajen samar da wadataccen abinci.
NLC na son karin albashi
A wani labarin, mun ruwaito cewa Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara tattaunawa da gwamnatin tarayya kan sabon mafi ƙarancin albashi.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce mafi ƙarancin albashin N70,000 da ake biya a yanzu bai ƙara wadatar ma'aikata ba sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa.
Ajaero ya bukaci ma'aikata su shirya domin sabuwar tattaunawa, yayin da wasu ƙungiyoyin farar hula suka yi kira da a ƙara mafi ƙarancin albashin zuwa akalla N500,000.
Asali: Legit.ng