Surukin kwankwaso ya lashe zaben fidda gwanin PDP a jihar Kano

Surukin kwankwaso ya lashe zaben fidda gwanin PDP a jihar Kano

A yau Talata, 2 ga watan Oktoba, 2018 an alanta Alhaji Abba Kabir Yusuf, a matsayin wannan zai yi takaran gwamnan jihar karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a shekarar 2019.

Zaben fitar da gwanin da aka gudanar a Lugard Avenue, gidan babban jigon jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bayan jami’an yan sanda sun hanasu zaben a gidan Sinima bisa ga umurnin kotu.

An kaddamar da wannan zaben ne cikin dare a gidan Kwankwaso

Shugaban zaben, Mr Ezeogu Emeka Onuoha, yayinda yake sanar da sakamakon zaben yace akalla mutane 4,130 ne aka tantance domin kada kuri’arsu a zaben.

KU KARANTA: PDP tayi zaben fiida gwaninta a gidan Kwankwaso cikin dare

Game da cewarsa, sakamakon zaben ya nuna cewa Abba Kabir Yusuf ya samu kuri’I 2,421, Alhaji Jafar Sani Bello ya samu kuri’u 1258, Muhammad Wali ya samu 167, yayinda Salihu Sagir Takai ya samu kuri’u 95.

Sauran yan takaran sune Ibrahim El Amin wanda ya samu kuri’u 51, sannan Akilu Sani Indabawa ya samu kuri’u 33.

Surukin kwankwaso ya lashe zaben fidda gwanin PDP a jihar Kano
Surukin kwankwaso ya lashe zaben fidda gwanin PDP a jihar Kano
Asali: Twitter

A jiya, Rundunar yan sanda sun tarwatsa zaben fidda gwani na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda bangaren Kwankwasiyya ke gudanarwa a Kano a jiya Litinin, 1 ga watan Oktoba.

Yan sanda sun hana daruruwan magoya bayan kwankwasiyya da suka taru a sakatariyar Lugard House shiga cikin ginin wanda suka yiwa kawanya tun da misalin karfe 06:00 na safe.

Babban sakataren kungiyar Kwankwasiyya na kasa, Kwamrad Auwal Muhammad ya bayyana cewa sun kasance a Lugard House domin a tantance tawagarsu da yan takararsu dake shirin zaben fidda gwani.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel