Yanzu Yanzu: Kotun koli ta soke hukuncin da aka yankewa Orji Kalu na shekaru 12 a gidan yari

Yanzu Yanzu: Kotun koli ta soke hukuncin da aka yankewa Orji Kalu na shekaru 12 a gidan yari

Kotun koli, a ranar Juma’a, 8 ga watan Mayu, ta soke hukuncin da aka yankewa tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor-Kalu na shekaru 12 a gidan yari.

Kotun kolin, a wani hukunci da kwamitin alkalai bakwai karkashin jagorancin Justis Amina Augie suka yanke, sun riki cewa babbar kotun tarayya ta Lagas ta yanke hukunci ba tare da hurumin yin hakan ba.

Wajen hukunta Kalu, da kamfaninsa na Slok Nigeria Limited da kuma tsohon daraktan kudi na jihar Abia, Jones Udeogu.

Yanzu Yanzu: Kotun koli ta soke hukuncin da aka yankewa Orji Kalu na shekaru 12 a gidan yari
Yanzu Yanzu: Kotun koli ta soke hukuncin da aka yankewa Orji Kalu na shekaru 12 a gidan yari Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Ta riki cewa Justis Mohammed Liman wanda ya yanke hukuncin bai kasance alkalin babbar kotun tarayyar ba a lokacin da ya yi zaman yanke hukunci kan wadanda ake karar.

Ana zarginsu da satan kudi kimanin naira biliyan 1.7 daga asusun jihar Abia.

A cewar kotun kolin, Justis Liman bai da ikon dawowa ya zauna a matsayin alkalin babbar kotu kasancewar an dauke shi zuwa kotun daukaka kara kafin wannan lokacin.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Gwamna ya yi umurnin yin gwanjon motocin da aka kama suna karya dokar kulle

Saboda haka, kotun kolin ta dage hukuncin da aka yankewa wadanda ake karan sannan ta yi umurnin sake sabon shari’a, jaridar Vanguard ta ruwaito.

A wani labarin kuma, mun ji cewa hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati, ta sha alwashin ci gaba da gudanar da harkokin da aka santa a kai duk da yadda annobar korona ta dagula al'amura a kasar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, EFCC ta sha alwashin ci gaba da shari'ar da shigar a kotuna daban-daban a kan wadanda ta ke zargi da yiwa tattalin arzikin kasar nan zagon kasa.

Babu shakka alamu sun nuna cewa, takunkuman da aka shimfida a kasar na hana fita da kuma kulle da manufar dakile yaduwar annobar korona, na iya kawo cikas ga yaki da cin hanci da rashawa da Hukumar EFCC ta sanya gaba.

Sai dai duk da hakan, Hukumar ta ce tangardar da cutar korona ta kawo ba za ta hana a ci gaba da gudanar da bincike gami da tankade da rairayen da ta ke yi a kan masu yiwa tattalin arzikin kasar ta'annati ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel