Mandela ya na cikin wadanda su ka tursasawa Obasanjo ya sauka – Inji Orji Kalu

Mandela ya na cikin wadanda su ka tursasawa Obasanjo ya sauka – Inji Orji Kalu

Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana yadda Marigayi tsohon Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Marigayi Nelson Mandela ya matsawa Olusegun Obasanjo ya hakura da maganar yin mulki sau 3.

Orji Kalu ya yi wannan bayani ne a wajen wani taro a Ranar Alhamis da ta gabata, 18 ga Watan Yuli, 2019. An shirya wannan taro ne domin tunawa da Marigayi Nelson Mandela a Birnin Abuja.

Kalu ya ce:

“Ina tuna tattaunar da mu ka yi da shi (Mandela), musamman a lokacin da mu ke kokarin tursasawa Olusegun Obasanjo ya yi watsi da yunkurin yi wa tsarin mulki kwaskwarima domin ya cibaba da mulki.”

Sabon Sanatan na jihar Abia ya ke cewa a wancan lokaci: “Mandela ya kira shugaba Olusegun Obasanjo a waya inda ya nuna masa cewa Afrika ba ta bukatar irin danyen aikin da ya ke shiryawa.”

KU KARANTA: An yi karin haske game da rikicin Shugaba Buhari da Obasanjo

“Wannan sa-baki da a ka yi ne ya yi tasiri a Najeriya a wancan lokaci, har a dalilin haka a ka yi zabe a 2007.” Sanata Kalu ya karasa jawabin na sa a wajen wannan taro na bikin tunawa da Mandela.

Ofishin Jakadancin kasar Afrika ta Kudu da ke Najeriya ne ta shirya wannan taro a jami’ar tarayya da ke Gwagwalada a cikin babban birnin tarayya Abuja. Bobby Roet ya samu halartar wannan biki.

Majiyar ta ce tsohon gwamnan na jihar Abia ya yi wannan jawabi ne a gaban shugabannin wannan jami’a watau Farfesa Abdul Rasheed Na-Allah, da kuma babban mataimakinsa Farfesa C.B.I Alawa.

A na zargin Obasanjo da yunkurin sake cigaba da darewa a kan mulki bayan ya cika wa'adi 2 a 2007. A karshe hakan ya gagara inda ya sauka daga kan mulki, har Marigayi Umaru 'Yaradua ya gaje shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel