Ebola: Gwamnatin Tarayya Ta Fayyace Gaskiya ga 'Yan Najeriya

Ebola: Gwamnatin Tarayya Ta Fayyace Gaskiya ga 'Yan Najeriya

  • Ministan Lafiya ya bukaci ’yan Najeriya kada su firgita kan bullar cutar Ebola, yana mai cewa gwamnati na da ƙarfin dakile ta
  • Wata mata da ta shigo Najeriya daga Uganda ta kamu da cutar, lamarin da ya sa aka fara bin diddigin mutanen da ta yi hulɗa da su
  • Gwamnati na aiki tare da Uganda da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) domin hana cutar yaɗuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan Lafiya, Dr Muhammed Ali Pate, ya bukaci ’yan Najeriya da kada su firgita kan bullar cutar Ebola a ƙasar.

Ministan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na da ƙwararrun hukumomi da kayan aikin da ake buƙata domin dakile yaɗuwar cutar.

An kwantar da hankalin 'yan Najeriya kan Ebola
Ministan lafiya, Mohammed Ali Pate na jawabi a wajen taro Hoto: Dr. Mohammed Ali Pate
Source: Twitter

Pate ya bayyana hakan ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, bayan ganawarsa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, a ranar Laraba, 21 ga watan Oktoban 2026, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

A gano jirgin da ya ɗauko mai ɗauke da cutar Ebola daga ƙasar waje ya shigo da ita Najeriya

Tun da farko, ministan ya tabbatar da cewa wata mata da ta shigo Najeriya ta jirgin sama daga Uganda ta kamu da cutar Ebola, bayan da aka yi mata magani a wani asibiti mai zaman kansa a Abuja.

Gwamnati ta fara daukar matakai

Da yake magana da manema labarai na fadar shugaban ƙasa, Pate ya ce Gwamnatin Tarayya na haɗin gwiwa da Uganda, tare da sauran hukumomin da abin ya shafa, domin shawo kan lamarin.

Ya bayyana cewa Najeriya na da hukumomi masu ƙwarewa wajen yaƙi da cutar, yana mai tunatar da cewa ƙasar ta taɓa samun nasarar dakile Ebola a shekarar 2014.

“Abin da zan iya gaya muku shi ne muna haɗin gwiwa da ƙasar Uganda, wadda ’yar’uwarmu ce a Afirka. Abu mafi muhimmanci shi ne mun gano wannan mutum guda da ya kamu da cutar."
“Muna bin diddigin mutanen da suka yi hulɗa da ita, sannan muna ɗaukar matakan kariya domin tabbatar da cewa cutar ba ta shiga cikin al’umma ta yaɗu ba."

Kara karanta wannan

Abin da cutar Ebola ke yi a jikin dan adam, da yadda za ku kare kan ku daga kamuwa

“Gwamnatin Tarayya na da ƙwararrun hukumomin da za su iya magance wannan matsala. Mun yi hakan a shekarar 2014, kuma muna da ingantattun cibiyoyin kula da lafiyar jama’a. Ya kamata ’yan Najeriya su kwantar da hankalinsu.” In ji shi.

An gargadi jama’a kan yaɗa jita-jita

Pate ya jaddada cewa duk da matakan da gwamnati ke ɗauka, ya kamata jama’a su kasance cikin shiri da taka-tsantsan, amma kada su firgita ko su riƙa yaɗa bayanan da ba su da tushe.

Ya bukaci ’yan Najeriya su riƙa bin sahihan bayanai daga majiyoyin lafiya da aka amince da su, maimakon yaɗa jita-jita da bayanan ƙarya.

Pate ya bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da sanar da jama’a sahihan bayanan da take samu a kullum.

Ministan ya ƙara da cewa Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) tana da tsarin kula da aukuwar irin wannan matsala, kuma jami’anta na aiki dare da rana.

A cewarsa, rundunar da aka kafa domin tunkarar cutar ma tana aiki, kuma akwai matakan da aka tanada waɗanda ke ba gwamnati kwarin gwiwar cewa Najeriya za ta iya shawo kan wannan matsalar lafiya ta jama’a.

“Kada a faɗa tarkon firgici”

Kara karanta wannan

Annoba mai alaka da kudaje ta barke a Gombe, an samu asarar rayuka

Ministan ya gargaɗi jama’a da kada su faɗa cikin abin da ya kira tarkon tsoro da firgici, yana mai jaddada cewa an gano mutum guda ne da ya shigo da cutar daga wata ƙasa, kuma ana ɗaukar matakan dakile ta.

“Kada mutane su faɗa cikin tarkon firgici ko tashin hankali. Mutum guda ne, kuma cutar ta shigo ne daga wata ƙasa. Muna ɗaukar matakan dakile ta, kuma za mu ci gaba da yin hakan."
“Idan yanayin ya sauya, za mu fito mu sanar da ’yan Najeriya.”
Ebola ta shigo Najeriya
Ana duba lafiyar wasu mutane saboda Ebola Hoto: Pius Utomi Ekpei
Source: Getty Images

Jirgin da ya dauko mai Ebola zuwa Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu bayanai game da matar da aka tabbatar tana ɗauke da cutar Ebola a Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.

Bayanai sun tabbatar da cewa an gano cewa ta shigo Najeriya ne ta jirgin saman Ethiopian Airlines a farkon watan Oktoban 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng