Fitaccen Malamin Addini Ya Bayyana Lokaci da Yadda Yake So Ya Mutu

Fitaccen Malamin Addini Ya Bayyana Lokaci da Yadda Yake So Ya Mutu

  • Fasto Enoch Adeboye, shugaban cocin RCCG, ya yi bayanin cewa zai so ya mutu a ranar Lahadi da ake bauta
  • A wani bidiyo a sahfin YouTube na RCCG, malamin addinin ya tuna cewa akwai wani kawunsa da ya mutu a bandaki ba tare da kowani radadi ko rashin lafiya ba
  • Malamin ya yi watsi da ra’ayin cewa mutane suna mutuwa ta rashin lafiya, inda ya yi addu’ar Allah yasa shi da duk wanda ke saurarensa su mutu ba tare da radadi, cuta ko rashin lafiya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ibafo, jihar Ogun - Fasto Enoch Adejare Adeboye, shugaban cocin RCCG, ya bayyana cewa zai so ya mutu ba tare da damuwa ko rashin lafiya ba.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Lauyoyin arewa fiye da 600 za su maka gwamnatin Tinubu a kotu, sun fadi dalili

Da yake magana a rana ta 3 na wani taron RCCG a dakin taro na cocin da ke jihar Ogun, malamin addinin ya ce zai so ya yi mutuwa irin ta wani kawunsa, wanda ya mutu a bandaki.

Fasto Adeboye ya ce yana so ya mutu ranar Lahadi
Malamin Addini Ya Bayyana Lokaci da Yadda Yake So Ya Mutu Hoto: Pastor Enoch Adejare Adeboye
Asali: Twitter

Fasto Adeboye yayi magana akan irin mutuwar da ta fi kowacce

A cewar Adeboye, kawunsa ya dawo daga coci a ranar da ya mutu sannan ya ci abincin rana mara nauyi wanda matarsa ta girka yayin da yake jiran a a gama hada masa sakwaran da aka girka masa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sai kawun nasa ya yanke shawarar zuwa bandaki lokacin da matarsa ke kicin tana hada masa sakwaran amma ya mutu a bandakin ba tare da rashin lafiya ko radadi ba.

Malamin addinin ya ce zai so ya yi mutuwar hankali kwance idan lokacinsa ya yi sannan ya yi addu'ar cewa duk wanda ke sauraronsa zai yi mutuwar hutu ba tare da kowani rashin lafiya ko cuta ba.

Kara karanta wannan

Yadda mutumin da ke aikin wanke bandaki a turai ya siya gida daga albashinsa, bidiyon ya yadu

Fasto Adeboye ya ba da labarin yadda kawunsa ya mutu

Ya ce:

"Na san wani zai ce, toh, idan ba mu yi rashin lafiya ba, toh ta yaya za mu taba mutuwa da zuwa aljannah? baka bukatar rashin lafiya don zuwa aljannah.
"Wani kawuna ya farka a ranar zuwa coci bauta Lahadi, ya tafi Coci, ya yi rawa kamar kowa, ya dawo gida, matarsa ta ba shi karin kumallo mara nauyi kafin ta shirya ainihin abincin - sakwara. Ta riga ta fara daka doya lokacin da kawuna ya yanke shawarar shiga bandaki.
"Bayan ta gama daka sakwatarn, sai ta kwankwasa kofar bandakin, da suka bude kofar, kawuna ya tafi. Babu rashin lafiya, babu ciwon kai, babu rardi. Idan Ubangiji ya yi kira, zan tafi a ranar Lahadi bayan abinci mai kyau na sakwara."

Abubuwa 3 da za su faru a 2024

A wani labari kuma, Prophet Abel Tamunominabo Boma ya ce akwai makirci da dama a shekarar 2024.

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a dandalinsa na YouTube, Prophet Boma ya ce harda Kiristoci cikin masu kulla makircin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel