Babban Faston Najeriya Ya Bayyana Abin Da Zai Faru Da Duk Wanda Ya Yi Wa Annabi Isa Batanci

Babban Faston Najeriya Ya Bayyana Abin Da Zai Faru Da Duk Wanda Ya Yi Wa Annabi Isa Batanci

  • Fasto E.A. Adeboye, shugaban cocin Redeemed Christian Church of God, RCCG, ya ce duk wanda ya yi wa Annabi Isa batanci zai gamu da fushin Allah
  • Fasto Adeboye ya yi wannan gargadin ne a matsayin martani ga wani mai sharhi kan harkokin yau da kulum, Daddy Freeze wanda ya ce mutanen Ogun sun koma bautan gargaji saboda Ubangiji ya gaza kare su daga yan bindiga
  • Malamin addinin ya bayyana cewa Ubangiji ne ke kare kowa kuma babu wanda zai mutu sai lokacin da aka diba masa ya cika

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Babban Faston cocin Redeemed Christian Church of God, RCCG, Fasto E.A. Adeboye, ya yi gargadin cewa duk wanda ya yi batanci ga Annabi Isa (AS) zai dandana fushin Ubangiji, rahoton The Punch.

Adeboye, wanda ya yi jawabi a taron RCCG na watan Yuli, ranar Juma'a/Asabar ya yi wannan maganan ne yayin martani kan hare-haren da ake kai wa coci-coci a sassan kasar.

Kara karanta wannan

A Zurfafa Bincike Kan Yaran Musulmi 21 Da Aka Ceto a Cocin ECWA Plateau, In Ji MURIC

Enoch Adeboye
Babban Faston Najeriya Ya Bayyana Abin Da Zai Faru Da Duk Wanda Ya Yi Wa Annabi Isa Batanci. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Religion Nigeria ta rahoto cewa a kalla mutum 40 ne yan darikar Katolika yan bindiga suka kashe a watan Yuni a Owo, Jihar Ondo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Makonni biyu bayan harin Owo, yan bindiga sun kashe mutum uku a wasu hare-haren a cocin Baptist da St Moses Catholic duk a karamar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.

Ya kuma yi martani ga mai tsokaci kan al'amuran yau da kulum a kafar sada zumunta, Daddy Freeze, wanda ya yi ikirarin cewa wasu sun koma bautan Ogun (Ubangijin Tsawa) ya tsine wa yan ta'addan da suka kai wa masu ibada hari a Owo saboda "Annabi Isa (AS)" bai amsa su ba.

Freeze, a watan da ta gabata ya rubuta, "Lokacin da suka kira bros J kuma bai amsa su ba fa? Mun yi watsi da addinan gargajiya na Afrika mun rungumi na turawa. Idan ba mu fara fada wa kanmu gaskiya ba kuma mun dauki tsaro da muhimmanci abin ba zai dena faruwa ba. Sakon Almasihu kauna ce kuma abin da a yanzu babu a Najeriya kenan."

Kara karanta wannan

Mai Wakar Zazu, Portable Ya Saduda Ya Mika Kansa Hannun Yan Sanda a Ogun

Martanin Fasto Adeboye

Da ya ke martani, Adeboye ya ce, "na fahimci wani mutum mai ban dariya ya ce wasu mutane suna kiran Ogun saboda Annabi Isa bai amsa su ba.
"Toh, akwai karin magana na Yarbawa, da ke cewa, bakin da dodon kodi ya yi amfani da shi ya yi batanci ga Ubangiji, bakin zai caki kasa. Daga yanzu, duk wanda ya sake yi wa Ubangiji batanci, za su dandani wutar Ubangiji mai Girma."

Malamin addinin ya cigaba da cewa, Ubangiji ne ke tsare mutane kuma babu wanda zai mutu sai lokacinsa ya yi.

'Batanci: Jakadiyar Birtaniya Ta Ce Dole a Hukunta Waɗanda Suka Kashe Ɗaliban Sokoto

A wani rahoto daban, Catriona Laing, Jakadar Birtaniya a Najeriya, ta yi alla wadai da kashe Deborah Samuel, wata dalibar Kwalejin Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto,kamar yadda ta rubuta a shafinta a Twitter.

Rahotanni sun ce dandazon fusatattun dalibai sun afka wa dalibar ne kan zarginta da furta maganganu na batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Asali: Legit.ng

Online view pixel