Shugaban Kasar Faransa, Macron Zai Shigo Najeriya, An Fadi Abin da Zai Kawo Shi

Shugaban Kasar Faransa, Macron Zai Shigo Najeriya, An Fadi Abin da Zai Kawo Shi

  • Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, zai kawo ziyarar aiki ta musamman Najeriya kafin ƙarshen watan watan Oktoban 2926
  • Ana sa ran Shugaba Macron zai ziyarci Najeriya a ranar 28 da 29 ga Oktoba, kamar yadda majiyoyin fadar shugaban ƙasa suka bayyana
  • Ziyarar za ta mayar da hankali kan ƙarfafa yarjejeniyoyin da Najeriya da Faransa suka cimma a ziyarar Bola Tinubu zuwa Faransa a 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, zai kawo ziyarar aiki ta musamman Najeriya kafin ƙarshen watan Oktoba, kamar yadda majiyoyin fadar shugaban ƙasa suka bayyana.

A cewar majiyoyin, idan babu wani sauyi da ak samu daga nan zuwa lokacin, an tsara ziyarar Shugaba Macron ne a ranakun 28 da 29 ga Oktoban 2026.

Shugaba Tinubu da Macron
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron lokacin da ya tarbi takwaransa na Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: anadolu
Source: Getty Images

Jaridar The Cable ta ce a watan Nuwamba 2024, Macron ya karɓi bakuncin Shugaba Bola Tinubu a ziyarar aiki ta musamman da ta ɗauki kwanaki uku.

Kara karanta wannan

Atiku ya magantu kan tsadar kayan noma, ya fadi mafita tare da sukar Tinubu

Yadda Bola Tinubu ya kai ziyara Faransa

Bayanai sun nuna cewa shugabannin biyu sun tattauna kan harkokin kuɗi, sauyin makamashi, ma’adinai masu daraja, kasuwanci da zuba jari, da sadarwa, da sauran batutuwa.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce ziyarar ta mayar da hankali ne kan “ƙarfafa alaƙar siyasa, tattalin arziki da al’adu da kuma samar da ƙarin damammaki na haɗin gwiwa”.

Shugaban Faransa zai shigo Najeriya

Ana sa ran ziyarar da Shugaba Macron zai kawo Najeriya za ta ƙara ƙarfafa yarjejeniyoyin da ƙasashen biyu suka cimma shekaru biyu da suka gabata a Faransa.

Majiyoyi sun shaida cewa jami’ai daga fadar shugaban Faransa sun fara isowa Najeriya domin “tattaunawa da takwarorinsu a nan tare da kammala shirye-shiryen” gabanin ziyarar Macron.

Wa’adin mulkin Macron na biyu kuma na ƙarshe zai ƙare a watan Mayun 2027. Ya ci gaba da kasancewa da kyakkyawar alaƙa da Tinubu tun bayan da ya zama shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya garzawa fadar babban sarki a Najeriya, an masa addu'o'i

Tinubu ya ziyarci Faransa aƙalla sau tara tun shekarar 2023, saboda dalilai daban-daban da suka haɗa da ziyarar aiki, hutun aiki da kuma tafiye-tafiye na kashin kansa.

Sabuwar alaƙar Afirka da Faransa

Marc Fonbaustier, jakadan Faransa a Najeriya da ECOWAS, ne ya fara bayyana cewa Macron zai ziyarci Najeriya a watan Yulin da ya gabata.

Jakadan ya ce ziyarar Macron za ta ba ƙasashen biyu damar duba ci gaban haɗin gwiwarsu na dabarun hulɗa da juna.

“Tare, shugabannin ƙasashenmu biyu za su tantance ci gaban taswirar shirye-shiryenmu tare da fayyace muhimman abubuwan da za su ƙulla alaƙarmu a shekaru masu zuwa," in ji Fonbaustier.
Shugaban Faransa.
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron yana jawabi a wurin taro Hoto: Mustafa Yalcinn
Source: Getty Images

Emmanuel Macron ya ziyarci Najeriya a 2018

Shugaba Macron ya ziyarci Najeriya na ƙarshe a matsayinsa na shugaban Faransa a watan Yulin 2018.

A lokacin, ya gana da marigayi tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, sannan ya kai ziyara New Afrika Shrine da ke Legas.

Shugaba Macron ya shirya wa Tinubu liyafa

Kun ji cewa shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya karbi bakuncin Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a wata liyafar dare na musamman a fadar Élysée da ke birnin Paris.

Ganawar ta kasance wani sabon mataki na hulda tsakanin shugabannin kasashen biyu yayin da Tinubu ke Faransa domin ci gaba da hutunsa na mako uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262