Kasar Canada: 'Yan Najeriya ne mafiya yawan masu zuwa mana qasa neman zaman din-dindin
- Kasar Canada tace yawan masu zuwa neman mafaka sun qaru sosai
- Daga Najeriya aka fi yi mata tururuwa don neman arziki
- Amurka, makociyar kasar ta rufe tata hanyar zurarar baqi cikin kasar

Asali: UGC
Bayan da Buhariyya ta matsa mutane a kasar nan, ba wai talakawa kadai ke guduwa ba, har ma masu hannu da shuni na tserewa domin sake sabuwar rayuwa a kasar da ke da arziki da ingancin rayuwa, da ma tsaro na lafiya da dukiya.
Kasar Canada mai sanyin bala'i, mai makwabtaka da Amurka, tace akasarin masu gudowa kasarta don neman sabuwar rayuwa daga Najeriya suke.
Najeriya dai na da jama'u da basu ma son juna, amma kuma duk talauci ya dabaibaye su, kuma kasashen da basu fiye so ba suke tserewa don neman mafaka.
DUBA WANNAN: Yadda DSS suka gano satar Oshiomhole
Alkalumma dai sun nuna 'yan Najeriya 6,000 ne a bara 2017, suka nemi maffaka ta din-dindin a kasar ta Canada, inda su kuma na Haiti suka kai 7,000.
Amurka ce tazo na uku, inda mutanen kasar keguduwa don haushin shugaban kasar su Donald Trump.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng