Fitaccen Jarumin Nollywood, Olu Jacobs Ya Rigamu Gidan Gaskiya?

Fitaccen Jarumin Nollywood, Olu Jacobs Ya Rigamu Gidan Gaskiya?

  • A yanzu ne muke samun labarin rasuwar fitaccen jarumin fina-finan Nollywood Olu Jacobs, wanda ya shafe shekaru yana fitowa a fim
  • An ce Olu Jacobs, miji ga Joke Silva, wanda ya yi fama da cutar nan ta mantau, ya rasu yana da shekaru 82 a duniya
  • Sai dai kuma, a wani bangaren, matarsa, Joke Silva ta ce mijinta na nan da ransa, labaran da ake yadawa na mutuwarsa ba gaskiya bane

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ana fargabar Nollywood ta sake yin rashin daya daga cikin tsofaffin jarumanta kamar yadda wani rahoto ya bayyana cewa fitaccen jarumi Oludotun Baiyewu Jacobs ya rasu.

Rahotannin rasuwar jarumi Olu Jacobs sun karade shafukan sada zumunta a ranar Lahadi, 30 ga watan Yuni wanda ya haifar da martani daga masu amfani da yanar gizo.

Kara karanta wannan

An sanya ranar da gwamna zai mika sandan girma ga sabon sarkin Ibadan

Olu Jacobs ya rasu
Allah ya yi wa Olu Jacobs rasuwa. Hoto: Jokes Silva
Asali: Instagram

Jarumi Olu Jacobs ya koma ga Allah?

Jaridar Tribune ta tattaro cewa Olu Jacobs, wanda da yawan matasa suka taso suna ganinsa a talabijin ya rasu kwanaki kadan da cikarsa shekaru 83 a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, a wani martani da matarsa Joke Silva ta yi, ta ce labaran da ake yadawa na mutuwar mijinta ba gaskiya ba ne domin har yanzu Olu Jacobs yana nan da ransa.

Da take magana da jaridar PM News a yammacin yau Lahadi, Joke Silva ta karyata jita-jitar, tana mai cewa "mijinta yana raye kuma yana samun sauki sosai."

Wannan dai shi ne karo na biyu da jita-jita game da mutuwar fitaccen jarumin, wanda ainihin sunansa Oludotun Baiyewu Jacobs, ke ta yawo a shafukan sada zumunta.

Ana alhinin mutuwar jarumin Nollywood

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin da masoyansa da ma masu kallon fina-finan Nollywood suka yi kan rasuwar jarumin.

Kara karanta wannan

Kano: Ana fargabar mutane sun mutu yayin da gini ya rufta kansu ana ruwan sama

capry_sunn:

"Sai mutuwa za ta raba mu" lallai Joke Silver ta rike wannan alkawarin."

comfort_gabriella1:

"Joke silver ta tsaya masa har mutuwa ta rabasu, aure nagari kenan, Allah ya sa ya huta."

b_uniqu.e:

"Matarshi ta zauna dashi har karshen rayuwarsa, Madam Joke silver abar alfahari ce, Allah ya sa ya huta."

ibrolee___:

"Ya samu mata 'yar amana, ta tsaya masa har zuwa karshen rayuwarsa."

Jarumar Nollywood, Stella ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Jarumar Nollywood, Stella Ikwuegbu ta rigamu gidan gaskiya a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni.

An bayyana cewa Stella ta mutu ne sakamakon ciwon daji da ya cinye kafarta kuma mutuwarta ta jefa mutane cikin jimami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.