Shekaru 7 da Ɗauke Dadiyata, El Rufai Ya Faɗi Gaskiyar abin da Ya Sani

Shekaru 7 da Ɗauke Dadiyata, El Rufai Ya Faɗi Gaskiyar abin da Ya Sani

  • Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya musanta hannun gwamnatinsa a batun batan Abubakar Idris, watau Dadiyata
  • El-Rufai ya bayyana cewa bincike ya nuna jami'an tsaro daga Kano aka aiko domin sace Dadiyata daga gidansa dake Kaduna
  • Tsohon gwamnan ya jaddada cewa shi bai ma ma san Dadiyata ba har sai da aka sace shi, don haka a tuhumi gwamnatin Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya musanta hannun gwamnatinsa a cikin lamarin ɓatan Abubakar Idris, wanda aka fi sani da suna Dadiyata.

Nasir El-Rufai ya nace cewa dukkan zarge-zarge da ke alaƙanta gwamnatinsa da dauke wannan matashi kuskure ne kuma ba su da ko kamshin gaskiya.

El-Rufai ya ce a tuhumi gwamnatin Kano kan batun bacewar Dadiyata
Abdullahi Ganduje (hagu), da Abubakar Idris, Dadiyata (tsakiya), da Malam Nasir El-Rufai (dama). Hoto: Hoto: @elrufai, @GovUmarGandujee, @ADCngcoalition (X)
Source: UGC

Batun bacewar Dadiyata a 2019

El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise News yau Juma'a, lokacin da aka yi masa tambaya game da lamarin batan Dadiyata.

Kara karanta wannan

El Rufai zai tsaya takarar shugaban Najeriya a 2027? Tsohon gwamna ya bada amsa

Dadiyata malami ne kuma mai sharhi a kafofin sada zumunta wanda wasu mahara suka sace shi a gidan sa dake Kaduna a shekarar 2019.

Hukumar Amnesty International ta bayyana hakan a matsayin 'batar da mutum da gangan', inda wasu masu suka ke zargin akwai sa hannun gwamnatin El-Rufai.

Duk da zarge-zargen da aka yi wa gwamnatin El-Rufai, da kiraye-kirayen kungiyoyin kare hakkin dan Adam da ma na 'yan Najeriya, har yanzu, bayan shekara bakwai, ba a san inda Dadiyata yake ba.

Martanin El-Rufai kan batan Dadiyata

Da yake martani ga masu zargin akwai sa hannun gwamnatinsa a batan Dadiyata, Nasir El-Rufai ya ce:

"Masu wannan zargi sun yi kuskure matuƙa. Abin da aka gaya muku ba gaskiya ba ne. Dadiyata ba mai sukar gwamnatin jihar Kaduna ba ne a lokacin.
"Shi babban mai sukar gwamnatin jihar Kano. Ku je ku duba dukkan abubuwan da ya riƙa rubutawa a shafukansa."

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa Dadiyata, wanda ɗan asalin jihar Kano ne, ya fi mayar da hankali ne wajen sukar Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje kawai.

Kara karanta wannan

"Sai mun tashi tsaye," Abin da El Rufai ya fadawa Atiku game da Tinubu a Abuja

Dangantakar Dadiyata da Gwamnatin Kano

Tsohon gwamnan na Kaduna ya kuma bayyana cewa:

"Ganduje ne matsalarsa. Ni ban ma san da shi ba har sai da aka sace shi, sannan na ji labarin abin da yake faruwa."

El-Rufai ya amince cewa Dadiyata yana zaune ne a Kaduna lokacin da aka sace shi, amma ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ba ta san da zamansa ba.

Nasir El-Rufai ya ce:

"Eh, yana zaune a jihar Kaduna, kuma haƙƙinmu ne mu kare shi. Amma ta yaya za mu kare mutumin da ba mu san shi ba?"

"A tambayi gwamnatin Kano" - El-Rufai

Ya ci gaba da iƙirarin cewa dukkan bayanan da aka tara lokacin bincike sun nuna cewa waɗanda suka sace Dadiyata sun fito ne daga jihar Kano.

Ya ƙara da cewa:

"Abin da muka ji daga iyalinsa shi ne maharan sun zo ne daga Kano. Idan za a yi wa wani tambaya, to a jefa tambayar ga jihar Kano."

Kara karanta wannan

Da sake: ADC ta dura a kan Tinubu saboda yunkurin kama El Rufa'i

Tsohon gwamnan na Kaduna ya kuma ce:

"Wannan lamari ba shi da wata alaƙa da gwamnatin jihar Kaduna. Shekaru uku bayan sace shi, wani ɗan sanda ya tabbatar da gaskiyar."
Malam Nasir El-Rufai ya ce babu hannun gwamnatinsa a sace Dadiyata da aka yi a Kaduna.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a dakin watsa shirye-shiryen Arise News. Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Iƙirarin tsohon dan sanda kan batan Dadiyata

Nasir El-Rufai ya kuma tuno yadda wani jami'in dan sanda ya fallasa abin da ya faru da Dadiyata, yana mai cewa:

"Dan sanda ya ya ce an aiko su ne daga jihar Kano domin su sace shi, kuma daga baya ya ji ba su kyauta ba. Ni iya abin da na sani kenan."

A ƙarshe, El-Rufai ya jaddada cewa bacewar Dadiyata ba matsala ce ta jihar Kaduna ba, illa dai kawai rikicin siyasa ne na wata jihar daban.

Kalli bidiyon tattaunawar da Imran Muhammad ya dora a shafinsa na X a nan kasa:

Abba ya yi alkawarin neman Dadiyata

A wani labarin can, mun ruwaito cewa, Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi alkawarin cewa ba za ta bari maganar dauke Dadiyata ta tafi a banza kawai ba.

Kara karanta wannan

Atiku ya ziyarci El Rufai cikin dare bayan ya sha da kyar a filin jirgin sama

A jawabin da ya yi bayan ya karbi ragamar mulkin jihar Kano a 2023, Abba Gida-Gida ya dauko maganar Dadiyata wanda aka sace tun a Agustan 2019.

Gwamnan ya ce har lokacin ba su manta da Dadiyata ba wanda masoyi ne kuma ‘dan tafiyar Kwankwasiyya, don haka za su binciki bacewarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com