Wani Gwamna ya bada umarni aka boye Dadiyata Inji Buba Galadima

Wani Gwamna ya bada umarni aka boye Dadiyata Inji Buba Galadima

Mun ji cewa tsohon Jigo na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Injiniya Buba Galadima ya fito ya na zargin gwamnatin Najeriya da kokarin takawa ‘yan adawan ta burki ko ta wani irin hali.

Buba Galadima ya bayyana cewa a dalilin a hana ‘yan adawa sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ake yi wa manyan masu fada-a-ji a kafafen yada labarai na zamani dauki dai-daya.

Babban ‘Dan adawar na gwamnatin APC ya zargi wani gwamna da laifin batar da Abubakar Abu Hanifah wanda aka fi sani da Dadiyata wanda Malamin jami’a ne mai sukar gwamnati mai-ci.

Ko da bai fadi sunan ainihin gwamnan ba, Galadima ya ce bisa umarninsa ne aka yi awon-gaba da Abubakar Idris watau Dadiyata a gidansa tun kwanaki. Yau wata guda kenan babu labarinsa.

KU KARANTA: Gaskiyar yadda aka kubutar da ‘Dalibai 3 na Jami’ar ABU Zariya ta fito

Jagoran hamayyar ya koka da halin da ake ciki na kassara Abokan hamayyar gwamnatin APC a Najeriya inda ya nuna cewa irin wannan mugun mataki da ake dauka ya sabawa dokar kasa

A wata hira da Injiniyan ya yi a gidan talabijin bayan ya yi dogon husufi, ya ce wannan Matashi da aka kama a boye har gida, bai aikata laifin komai ba. A nan ne a ka yanke masa hanzari a hirar.

Wannan Matashi da aka sace tun a farkon Watan Agusta ya na cikin wadanda su ka matsawa gwamnatin APC lamba musamman a kafafen sadarwa na zamani na Tuwita da sauransu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel