A sanar damu wurin da aka kai Dadiyata, sakon matasan PDP zuwa ga Buhari

A sanar damu wurin da aka kai Dadiyata, sakon matasan PDP zuwa ga Buhari

-Kungiyar matasan PDP sun gudanar da zanga-zanga a Abuja a kan Abubakar Idris da aka yi gaba da shi tun ranar 8 ga wata

-Kungiyar ta nemi gwamnati ta yi mata bayanin wurin da aka kai wannan matashin wanda aka fi sani da suna Dadiyata

Kungiyar matasan jam’iyyar PDP a ranar Alhamis 15 ga watan Agusta sun roki Shugaba Buhari a kan a sanar da su inda aka kai Abubakar Idris wanda aka fi sani da Abu Hanifa Dadiyata.

Ana zargin jami’an tsaron DSS ne su kayi gaba da shi ranar Juma’a 8 ga watan Agusta zuwa wani wurin da ba a san ko ina bane.

KU KARANTA:Jerin sunayen sabbin kwamishinonin Jihar Oyo 14 da ma’aikatunsu

Kungiyar matasan ta bayyana Dadiyata a matsayin daya daga cikin wadanda ke yawan magana game da lamuran gwamnatin Najeriya.

Matasan wadanda suka shirya wata zanga-zanga a gaban Unity Fountain otel dake Abuja, sun bayyana cewa ko dai hukumar DSS ta sako dan uwansu ko kuma a kai shi gaban kotu.

Dauke a hannun matasan kwalaye inda suka rubuta ‘Ina Dadiyata’. A cewar kungiyar matasan wannan abinda da hukumar DSS tayi ya saba doka saboda an tsare shi sama da kwana biyu.

Matashin wanda yayi fice kwarai da gaske a shafukan sada zumunta wurin bayyana ra’ayinsa dangane da siyasar Najeriya, an nemi shi an rasa tun ranar 8 ga watan Agusta.

Bugu da kari, Abubakar Idris malami ne a Jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutsenma cikin Jihar Katsina. Tun daga ranar Juma’a 8 ga wata har yanzu babu labarin wurin da Dadiyata yake.

Asali: Legit.ng

Online view pixel