Sojojin da Suka Jagoranci Juyin Mulki da Yadda Suka Yi Nasara a Tarihin Najeriya
Bayan rade radin shirya wa shugaba Bola Ahmed Tinubu juyin mulki, Legit Hausa ta hada rahoto na musamman kan lokutan da aka yi juyin mulki a Najeriya.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A makon da ya wuce aka fara rade radin cewa wasu sojoji sun shirya yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu juyin mulki a Najeriya.
A tarihin Najeriya, an yi wa gwamnatocin farar hula har da na soja juyin mulki saboda wasu zarge zarge da nufin a hambarar da su.

Source: Getty Images
A wannan rahoton, Legit Hausa ta hada rahoto na musamman kan lokutan da aka yi juyin mulki a tarihin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Juyin mulkin farko a 1966
Manjo Patrick Chukwuma, wanda aka fi sani da Kaduna Nzeogwu, yana cikin jagororin juyin mulki na farko a Najeriya a ranar 15 ga Janairu 1966, bayan shekaru shida da samun 'yancin kai.
Wannan juyin mulki ne ya yi sanadiyyar mutuwar Firaminista Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa da Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello.

Source: Depositphotos
Bayan haka ne Manjo Aguinyi Ironsi ya hau mulkin soji na tsawon wata shida kafin a hamɓarar da shi.
Nzeogwu ya shiga hannun hukuma, aka daure shi a gidan yarin Kirikiri sannan aka mayar da shi Aba. An sake shi a 1967 lokacin yaƙin Biafra, amma an kashe shi a Nsukka a ranar 29 ga Yuli 1967 lokacin yakin basasa.
2. Juyin mulki na 2 a 1966
Wata shida bayan juyin mulkin farko, Laftanar Kanal Murtala Ramat Muhammad ya jagoranci juyin mulki.
Bayan juyin mulkin ne Yakubu Gowon ya zama shugaban ƙasa. Murtala ya ci gaba da aikin soja har ya zama shugaban ƙasa daga baya.

Source: Getty Images
Sai dai an kashe shi a wani yunƙurin juyin mulki da Bukar Suka Dimka ya jagoranta a ranar 13 ga Fabrairu 1976.
3. Juyin mulkin 1975 da ya kawo Murtala
Bincike ya nuna cewa a ranar 29 ga Yuli 1975, ƙananan sojoji suka kitsa juyin mulki ba tare da asarar rai ba.

Source: Depositphotos
Joseph Nanven Garba ne ya sanar da shi a gidan rediyo, inda ya bayyana Murtala Ramat Muhammad a matsayin sabon shugaban ƙasa da Olusegun Obasanjo a matsayin mataimaki.
Wannan juyin mulki ya faru ne lokacin da shugaban lokacin, Yakubu Gowon yake a taron ƙungiyar OAU a Uganda.
4. An yi juyin mulki a shekarar 1983
A ƙarshen shekarar 1983, sojoji suka kifar da gwamnatin Alhaji Shehu Shagari, kuma Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa.

Source: Getty Images
Ba a bayyana jagoran juyin mulkin kai tsaye ba, amma sunayen da suka fito sun haɗa da Kanal Tunde Ogbeha da Birgediya Ibrahim Baƙo, wanda ya mutu lokacin harin fadar shugaban ƙasa.
BBC Hausa ta rahoto cewa duk da zargin cewa marigayi Muhammadu Buhari na da hannu, ya musanta cewa yana da masaniya a kai.
5. Juyin mulki a 1985 ya kawo IBB
A ranar 27 ga Agusta 1985, Ibrahim Badamasi Babangida ya jagoranci juyin mulki, inda ya hamɓarar da Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan
Biki bidiri: An daura auren fitaccen jarumin fim a Najeriya ana cikin tafiya a jirgi

Source: Getty Images
A lokacin, Babangida ne shugaban sojojin ƙasa. Ya mulki ƙasar har zuwa 1993, lokacin da ya amince ya sauka daga mulki.
Yayin da yake ofis ne aka yi yunƙurin juyin mulkin Gideon Orkar a 1990 wanda bai yi nasara ba.
6. Juyin mulki na karshe a 1993
A ranar 17 ga Nuwamba 1993, Manjo Janar Sani Abacha, wanda a lokacin ya ke ministan tsaro, ya hamɓarar da gwamnatin Ernest Shonekan da Ibrahim Babangida ya kafa.
Wannan juyin mulki bai jawo zubar da jini ba. Abacha ya mulki ƙasar daga 1993 har zuwa mutuwarsa a ranar 8 ga Yuni 1998.

Source: Twitter
Bayan rasuwarsa, Janar Abdulsalami Abubakar ya karɓi mulki sannan ya miƙa wa Olusegun Obasanjo a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a ranar 29 ga Mayu 1999.
Juyin mulkin da ba su yi nasara ba
Akwai yunkurin juyin mulkin da ba su yi nasara ba kuma aka cafke wadanda ake zargi.

Kara karanta wannan
Tuna baya: Lokacin da aka yi yunkurin kifar da gwamnatin Obasanjo a mulkin farar hula
Har juyin mulkin farko da aka yi a farkon 1966, an yi nasarar canza gwamnati amma ba wadanda suka yi niyya bane suka iya hawa mulki.
1. Yunkurin juyin mulkin Bukar Dimka
A ranar 13 ga Fabrairu 1976, Laftanar Kanal Bukar Dimka ya jagoranci yunƙurin juyin mulki wanda ya kai ga kisan Murtala Muhammad.
Sai dai ba a bar juyin mulkin ya yi tasiri ba, domin an kama shi makonni uku bayan haka a Abakaliki kuma an yanke masa hukuncin kisa tare da wasu abokan sa guda shida a ranar 15 ga Mayu 1976.
2. Yunkurin juyin mulkin Gideon Orkar
Punch ta wallafa cewa Manjo Gideon Orkar ya jagoranci yunkurin juyin mulkin da aka yi a ranar 22 ga Afrilu 1990 domin kifar da gwamnatin Babangida.

Source: Getty Images
Duk da cewa ya samu damar kai farmaki a Barikin Dodon, Babangida ya tsira da taimakon abokinsa, Janar Sani Abacha.
Bayan gazawar juyin mulkin, an kama Orkar da wasu, inda aka yanke musu hukuncin kisa a ranar 27 ga Yuli 1990.
Ana bincike kan zargin juyin mulki a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa ana rade radin cewa ana bincike kan juyin mulkin da aka so yi wa shugaba Bola Tinubu.
Rundunar tsaron Najeriya karkashin Janar Christopher Musa ta karyata cewa an yi yunkurin juyin mulki a kasar.
Sai dai duk da haka, wasu bayanan sirri sun nuna cewa ana binciken wani tsohon gwamna kan zarginsa da hannu a yunkurin juyin mulkin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


