Yau a Tarihi: Kisan Sardauna, Tafawa Balewa, da abubuwa 2 da suka faru

Yau a Tarihi: Kisan Sardauna, Tafawa Balewa, da abubuwa 2 da suka faru

A cikin shirinmu na waiwaye adon tafiya, muna kawo muku abubuwan da suka faru masu muhimmanci a tarihin kasarmu Najeriya.

A ranar irin ta yau 15 ga watan Junairu akayi juyin mulki na farko a Najeriya.

A ranar aka kashe Firam ministan Najeriya na farko, Abubakar Tafawa Balewa; Firimiyan Arewa, Ahmadu Bello Sardauna; ministan kudi, Festus Okotie-Eboh da Samuel Ladoke Akintola.

Sauran manyan Sojojin Arewan da aka kashe sune Laftana Pam, Laftana Largema, Kanal Kur, da Birgdiya Maimalari.

Sojoji Inyamurai sun kashe wadann

an shugabannin ne domin baiwa Janar Aguiyi Ironsi daman zama shugaban kasa.

Sakamakon haka, Sojojin yan Arewa suka dau fansa inda suka kashe Sojoji Inyamurai da masu farar hula kuma hakan ya sabbaba yakin basasan 1967.

Ga jerin abubuwan da suka faru:

Jan 15 1966: An yi juyin mulki na farko a Najeriya

Jan 15 1966: Kaduna Nzeogwu da Emmanuel Ifeajuna suka jagoranci juyin mulki inda suka kashe Firam Minista Tafawa Balewa da manyan jami'an gwamnati

Jan 15 1970: Mayakan Biyafara sun mika wiya bayan shekaru biyu da rabi ana fafatawa a yakin Basasa

Yau a Tarihi: Kisan Sardauna, Tafawa Balewa, da abubuwa 2 da suka faru
Yau a Tarihi: Kisan Sardauna
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel