Gowon ya bayyana halin da ya tsinci kansa lokacin da ya zama shugaban Najeriya yana dan shekara 31
- Tsohon shugaban kasa na mulkin soja a Najeriya Yakubu Gowon ya ce fadi yadda ya ji a lokacin da ya zama shugaban ƙasa
- Janar Yakubu Gowon mai ritaya ya ce ya firgita a lokacin da ya zama shugaban ƙasa yana da shekaru 31
- Ya ce bai taba tunanin zai zama shugaban ƙasa ba shi burinsa kawai ya zama soja mai nagarta da zai yi wa kasarsa aiki
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja a Najeriya, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) ya ce ya firgita a lokacin da ya zama shugaban kasa a ranar 1 ga watan Agusta yana da shekaru 31.
A cewar wata sanarwa a ranar Juma'a mai taken "Yadda na zama shugaban ƙasa ina da shekaru 32" tsohon shugaban ya yi jawabi a wurin taron da aka yi ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo mai nuna bidiyo da sauti da gidauniyar ANISZA ta shirya.
DUBA WANNAN: Nigeria@60: Ɗan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durƙusa yana gaishe da mara lafiya
Gidauniyar ta yi shirya taron ne don bikin cikar Najeriya shekaru 60 da samun ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Gowon ya zama shugaban Najeriya mafi ƙarancin shekaru a lokacin da ya zama shugaba mukin soji a ranar 1 ga watan Agustan 1966 kafin ya cika shekaru 32 a ranar 19 ga watan Oktoba.
Ya yi mulki daga shekarar 1966 zuwa 1975.
"Na firgita a lokacin da na kama mulki a matsayin shugaban kasa. Ban taɓa tunanin zan zama shugaban ƙasa ba, abin ya faru ne kawai," Gowon ya ce.
Sanarwar ta kara da cewa, "Tsohon shugaban kasar ya tattauna da matasan Najeriya da suka hallarci taron ta fasahar intanet inda aka tattauna batutuwa da suka shafi zaman lafiya da haɗin kai tsakanin ƴan Najeriya da ma duniya.
KU KARANTA: Kotu ta bawa musulmi damar zuwa Sallah a lokutan aiki a Sweden
"Dattijon ya yi waiwaye kan wasu abubuwa da suka faru a rayuwarsa kuma ya bawa matasan shawarwari kan yadda za su gina kansu da ƙasa.
"Cikin mahalarta taron akwai wasu yara ƴan makaranta da mambobin ƙungiyar makarantar ANISZA da suka zaune kusa da wacce ta shirya taron mai suna Isioro yayin da ta ke tattaunawa da tsohon shugaban ƙasar.
"Gowon ya sake jaddada imaninsa game da hadin kan Najeriya inda ya ce za a iya zama lafiya duk da banbancin addini da kabila."
A wani rahoton, gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Alhamis ya sanar da sakin fursunoni 25, rage wa'adin wasu ciki har da waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa da aka sauya musu zuwa ɗaurin rai da rai.
Gwamnan ya sanar da hakan ne cikin jawabinsa na bikin ranar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ƴanci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng