Yadda aka kashe General Murtala Muhammad
- An kashe Janar Murtala a ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 1976
- Lt. Col. B Dimka shiya jagoranci kisan tsohon shugaban kasar
- Ya samu hadin kan wasu manyan Najeriya da kuma kananan hafsoshin sojoji domin tsara juyin mulkin
Ranar 13 ga watan Fabrairu na shekarar 1976, na daga cikin ranakun da suka canja tarihin Najeriya saboda a wannan ranar ce aka yi yunkurin kifar da gwamnatin Marigayi Janar Murtala Ramat Mohammed, amma a karshe ba a samu nasarar juyin mulkin ba, sai dai shi ya rasa ransa bayan da bijirarrun sojoji a karkashin jagorancin Lt. Col. B. Dimka.
DUBA WANNAN: Da alamun hukumar NEDC zata kawo sauyi ga mutanen Arewa maso gabas
A lokacin da aka kama Dimka kuma aka yanke masa hukuncin kisa, ya zayyana yadda suka shirya juyin mulkin da kuma yadda suka samu nasarar kashe Murtala inda ya nuna cewa tun a watan Janairu na shekarar 1976 suka fara shirya makarkashiyar, bayan ya sadu da wasu manyan mutane wanda ya hada har da Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Yakubu Gowon wanda a lokacin yake gudun hijira a London bayan an tunbuke shi daga mulki. Dimka ya ci gaba da cewa, a lokacin ya samu hadin kan kananan hafsoshin soja bisa yadda ya tsara tun farko na kin saka duk wani babban hafsan soja cikin shirin juyin mulkin, inda ya kara da cewa sun tuntubi Janar Bisalla wanda ya ba su karfin guiwar cewa duk abin da zai faru kada su janye batun kifar da mulkin, inda ya nuna masu cewa yana cikin majalisar koli ta mulkin soja amma a duk lokacin da za a yi zama sai a tura shi wani aiki. Dimka ya kara da cewa sun tsara kashe manyan hafsoshin soja bayan shi kansa Shugaban Kasa, Murtala Mohammed da Mataimakinsa, Cif Olusegun Obasonjo kuma wadannan manyan sojojin sun hada da, Janar T. Y Danjuma, Kanal Ibrahim Badamasi Babangida, Kanal Bajowa, Kanal Mohammed, Kwamandan rundunar Shiyyar Sokoto, Kanal Ibrahim Taiwo sai Kanal Jemibewon da ke rike da rundunar Ibadan sai Kanal Abdullahi da ke jagorantar rundunar shiyyar Jos.
Dimka ya fayyace yadda suka samu nasarar kashe Murtala inda ya ce a Ranar 13 ga watan Fabrairu na shekarar 1976 shi da wasu daga cikin bijirarrun sojojin sun yi kwantan bauna a daidai kan titin George da ke Legas inda Murtala zai bi ya wuce daga barikin 'Dodon Barracks', wanda a lokacin nan ne Fadar gwamnatin mulkin soja, inda ya ce a lokacin da motar da ke dauke da Murtala ta doso inda suke labe sai Kyaftin Maliki ya ba su alamar tasowar tawagar Shugaban kasar wanda a cewar Dimka a lokacin da motar ta wuce inda yake bai ganta ba, saboda a lokacin yana Magana da wasu sai da aka ankarar da shi. Dimka ya ci gaba da cewa, sun bi motar daga baya inda suka datse ta a daidai wani gidan man fetur da ke titin 'Bank Road' wanda daga nan ne, suka fara harbi kuma suka samu nasarar kashe Murtala Mohammed da dogarinsa, Lt. Akintunde Akinsehinwa da kuma direban motarsa.
Dimka ya ce bayan sun kashe Murtala, ya tafi gidan rediyo ya bayar da sanarwar juyin mulki. Sai dai kuma an samu nasarar murkushe juyin mulkin inda aka yankewa Dimka shi da wasu mutane bakwai hukuncin kisa kuma aka zartar da hukuncin a ranar 15 ga watan Mayu na shekarar 1976, kuma a lokacin har da Gwamnan jihar Benue Plateau, Joseph Gomwalk.
Allah Ya Jikan Murtala Ya yi masa rahama.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng