EFCC Ta Gurfanar da Tsohuwar Shugabar Hukumar NSITF, Ana Zargin Ta Wawure N1bn

EFCC Ta Gurfanar da Tsohuwar Shugabar Hukumar NSITF, Ana Zargin Ta Wawure N1bn

  • EFCC ta gurfanar da tsohuwar shugabar NSITF, Ngozi Olejeme, a kotu kan tuhume-tuhumen karkatar da N1bn da safarar kudin haram
  • Hukumar ta zargi Mrs Ngozi da karkatar da N321.6m da kuma dala miliyan biyu yayin da take shugabantar NSITF daga 2012 zuwa 2015
  • Sai dai, Ngozi ta musanta aikata tuhume-tuhume tara da ake yi mata, inda alkalin kotun Emeka Nwite ya dage shari'ar zuwa Nuwamba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohuwar shugabar hukumar NSITF, Ngozi Olejeme, gaban babbar kotun tarayya Abuja.

Tshohuwar shugabar hukumar asusun inshorar ci gaban al'umma ta na fuskantar tuhume-tuhumen karkatar da N1bn

EFCC ta gurfanar da tsohuwar shugabar hukumar NSITF a kotu kan zargin rashawa
Hoton tsohuwar shugabar NSITF, Ngozi Olejeme da EFCC ta gurfanar da ita kotu. Hoto: @officialEFCC
Source: Twitter

An gurfanar da tsohuwar shugabar NSITF

A sanarwar da aka wallafa a shafin EFCC na X, an bayyana cewa an gurfanar da Ngozi ne a ranar Laraba, kan tuhume-tuhume tara.

Kara karanta wannan

Amupitan: Lauyoyi na shirin kawo cikas ga tabbatar da nadin shugaban INEC a majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuhume-tuhumen da ake yi mata sun hada da karkatar da kudi, canjawa, saye da mallakar kudaden da aka samo ta haram.

A cewar EFCC, ana zargin Ngozi ta karkatar da kudade masu yawa, wadanda mallakin hukumar NSITF ne daga 2012 zuwa 2015, lokacin tana kan kujerarta.

Wani bangare na takardar tuhume-tuhumen da EFCC ta gabatar a kotu na cewa:

"Cewa ke Mrs. Ngozi Olejeme, yayin da kike shugabantar hukumar NSITF, a 2012 a Abuja, kin karkatar da N321,600,000 da aka sanya a asusun kamfanin Adin Miles na Sterling a ranar 9 ga Fabrairu, 2012, alhalin kin san cewa an samu wannan kudi ta haramtacciyar hanya.
"Wannan abu da kika aikata ya ci karo da sashe na 15(2)(b) kuma an tanadi hukuncinsa karkashin sashe na 15(3) na dokar yaki da safarar kudi da aka samar a 2011 (aka sabunta a 2012."

NSITF: EFCC na zargin an karkatar da $2,000,000

Kara karanta wannan

An gano tsofaffin shugabannin Najeriya 3 da ba su halarci taron majalisar koli ba

Hakazalika, hukumar EFCC ta zargi Ngozi da karkatar da miliyoyin daloli, yayin da a cikin takardar karar, hukumar ta shaida wa kotu cewa:

"Cewa, ita Mrs. Ngozi Olejeme, lokacin tana shugabar hukumar NSITF a ranar 9 ga Fabrairu, 2012 a Abuja, ta samarwa wani Chuku C. Eze dala miliyan biyu domin ya canja mata zuwa kudi, matsayin kudin da za a sanya a asusun Adin Miles, alhalin kin san cewa an samu kudin ta haramtacciyar hanya.
"Wannan aiki ya ci karo da sashe na 18(c) kuma yana da hukunci a karkashin sashe na 15(3) na dokar yaki da safarar kudi ta 2011 da aka sabunta a 2012."
EFCC ta gurfanar da tsohuwar shugabar hukumar NSITF a kotu kan zargin rashawa
Hoton jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a bakin aiki. Hoto: @officialEFCC
Source: UGC

An bada belin tsohuwar jami'ar gwamnati

Sai dai, bayan karanta mata dukkanin tuhume-tuhumen, Ngozi ta musanta aikata su, lamarin da ya sa lauyan EFCC, Emenike Mgbemele ya roki kotu ta sanya lokacin fara shari'ar.

Hukumar EFCC ta shaida ma kotun cewa idan aka sanya lokacin fara shari'ar, to za ta gabatar da shaidu 14 da za su tabbatar da zarge-zargen da ake yi wa Ngozi.

Sai dai, Emeka Ogboguo, lauyan wacce ake kara ya shaida wa kotun cewa akwai bukatar ba da bekin Ngozi da aka gabatar, do haka ya nemi alkalin ya amince da ba da belin.

Kara karanta wannan

IBB, Abdulsalami sun halarci taron majalisar koli, karon farko babu Buhari

Emeka Nwite, alkalin kotun, ya ba da umarnin a ba da belin wacce ake kara ga lauyanta, sannan ya daga shari'ar zuwa 17 ga Nuwamba, domin sauraron bukatar beli.

EFCC ta kwace kadarori 46 mallakin Ngozi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin kwace kadarori 46 mallakin tsohuwar shugabar NSITF, Ngozi Olejeme.

A jikin takardar umarnin da aka ba hukumar EFCC, kotun ta ce a kwace kadarorin da suka hada da gidaje a jihohin Delta, Enugu, Bayelsa da babban birnin tarayya.

Ana zargin Ngozi ta hada baki ne da tsohon shugaban NSITF, Mr Umar Munir Abubakar suka karkatar da sama da Naira biliyan 69 daga asusun gwamnati.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com