Yanzu-yanzu: FG ta kafa kwamitin bincike a kan NSITF

Yanzu-yanzu: FG ta kafa kwamitin bincike a kan NSITF

- FG ta kaddamar da kwamitin bincike a kan zargin badakalar wasu kudade da ake wa asusun bada tallafin inshora na kasa

- Ministan kwadago da aikin yi, Dr Chris Ngige, ya sallami shugabannin hukumar NSITF saboda shaidu a kan damfara da ya bayyana a kansu

- Kwamitin zai samu shugabancin Ibraheem Khaleel

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin bincike a kan zargin badakalar wasu kudade da ake wa asusun bada tallafin inshora na kasa (NSITF).

A cikin kwanakin nan, ministan kwadago da aikin yi, Dr Chris Ngige, ya sallami shugabannin hukumar NSITF saboda shaidu a kan damfara da ya bayyana a kansu.

Kwamitin zai samu shugabancin Ibraheem Khaleel. Ana sanya ran za su kai rahoton ga gwamnatin tarayya a cikin sati uku.

Yanzu-yanzu: FG ta kafa kwamitin bincike a kan NSITF
Yanzu-yanzu: FG ta kafa kwamitin bincike a kan NSITF Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ngige ne ya rantsar da kwamitin binciken na mutum 10 a babban ofishin NSITF a Abuja a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ministan ya samu wakilcin babban sakataren ma'aikatar, William Alo.

KU KARANTA KUMA: Kaduna: Ku fallasa duk wanda kuka san yana da hannu a rikici - El-Rufai ga shugabanni

A wani labari na daban, kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya ce kwamitin bincike na fadar shugaban kasar ya tsare dakataccen shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ne don tabbatar da cewa ba a taba takardu masu muhimmanci ba.

Adesina ya sanar da hakan ne a wani shirin gidan talabijin na Channels mai suna "siyasarmu a yau".

Hakazalika, lauyan Magu, Rosin Ojaomo, ya ce idan mai shari'a Salami ya gano cewa Magu bai aikata ko daya daga cikin zargin da ake ba, toh shugaban kasa ya mayar da shi kujerarsa.

Sai dai, Adesina ya ce shi ba lauya bane balle ya san ko daidai bane abinda kwamitin yayi na tsare Magu har tsawon kwanaki 10.

Amma ya ce akwai yuwuwar wasu takardu masu alaka da binciken ne basu so a taba yayin da suke aikinsu.

Ya ce kafin a gayyaci Magu, kwamitin ya yi zama na makonni masu tarin yawa don tattaunawa a kan zargin rashawar tare da duba ko akwai bukatar ganin shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel