EFCC ta kwace gidaje 46 mallakar darektan kamfen din Jonathan

EFCC ta kwace gidaje 46 mallakar darektan kamfen din Jonathan

- EFCC ta tsare tsohuwar direktan yakin neman zaben tsohon shugaba Goodluck Jonathan, Ngozi Olojeme

- Hukumar ta EFCC ta kuma kwace wasu kadarori 27 daga hannun Ngozi Olojeme da ake zargin ta mallake su ta haramtaciyar hanya

Wata babban kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umurnin kwace wasu kadarori 46 mallakar Dr. Ngozi Olojeme, mataimakiyar ciyaman na kwamitin kudi na kamfen din tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a zaben shekarar 2015.

Punch ta ruwaito cewa takardar umurnin kotun ya nuna gidaje da yawa a jihohin Delta, Enugu, Bayelsa da babban birnin tarayya, Abuja.

EFCC ta kwace gidaje 46 mallakar darektan kamfen din Jonathan
EFCC ta kwace gidaje 46 mallakar darektan kamfen din Jonathan
Asali: Twitter

Kadarorin wadda adadin ya kai 27, sun hada da ginin banki, ofisoshi da gidajen zama da ake kan ginawa da kuma filaye da dama wadanda ba a fara gini a kan su ba.

Olejeme, wadda ita ce Ciyaman din Nigeria Social Insurance Trust Fund tana fuskantar (NSITF) tuhuma ne da aikata laifin hadin baki, karkatar da kudade, sata da kuma amfani da ofishinta ta hanyar da ba ta da ce ba.

Ana zargin tsohuwar ciyaman din ta hada baki ne da tsohon shugaban NSITF, Mr Umar Munir Abubakar inda suka karkatar da sama da Naira biliyan 69 daga asusun gwamnati zuwa aljihun su ta hanyar bayar da kwangilar bogi ga wasu kamfanoni.

Olojeme kuma mata ce ga tsohon babban mai tsaro na Jonathan, Felix Obuah. Ta tsere daga Najeriya ne bayan shugaba Muhammadu Buhari ya sallame ta daga aiki a shekarar 2015.

Wadda ake tuhumar ta amsa gayyatar hukumar yaki masu yiwa arzikin kasa ta'annti EFCC ne a ranar Litinin amma sai aka tsare ta.

Kamar yadda takardun kotun suka nuna, ana zargin Olojeme da wasu direktocin kamfanin NSITF ne da laifin karkatar da biliyoyin kudade na albashi da alawus din ma'aikatan su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: