Ragin ₦38,000: An Ji Babban Gatar da Tinubu Ya Yi wa Masu Ciwon Koda a Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da rage kuɗin wanke ƙoda daga ₦50,000 zuwa ₦12,000 a asibitocin tarayya da ke fadin ƙasar
- Daniel Bwala ya ce an fara aiwatar da shirin a manyan asibitocin tarayya, domin kawo sauƙi ga masu fama da cututtukan ƙoda
- Wasu ‘yan Najeriya sun soki matakin, inda suka ce ragin ba zai kawo wani sauki ba tun da ana yin wankin koda ne sau 2-3 a mako
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya amince da rage kuɗin wankin ƙoda daga ₦50,000 zuwa ₦12,000 a asibitocin tarayya a faɗin ƙasar nan.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada manufofi, Daniel Bwala, ne ya bayyana hakan a shafukan sada zumunta a ranar Litinin.

Source: Twitter
Tinubu ya rage kuɗin wankin ƙoda

Kara karanta wannan
'Gwamnan CBN na iya fin shugaban kasa albashi,' Gwamnati za ta kara wa jami'ai kudi
A shafinsa na X, Bwala ya rubuta cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Da wannan mataki, an rage kuɗin kowane wankin ƙoda daga ₦50,000 zuwa ₦12,000 kacal, abin da zai kawo sauƙi ga dubban ƴan ƙasa da ke fama da cututtukan ƙoda.”
A cewar Bwala, an riga an fara aiwatar da tallafin a manyan asibitocin tarayya a dukkanin shiyyoyi guda shida.
Asibitocin sun haɗa da FMC, Ebute-Metta, Legas; FMC, Jabi, Abuja; Asibitin jami'ar Ibadan UCH; da FMC, Owerri.
Sauran sun haɗa da Asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri (UMTH), Maiduguri; FMC, Abeokuta; da Asibitin koyarwa na jami'ar Lagos (LUTH), Legas.
Akwai kuma FMC, Azare; Asibitin koyarwa na jami'ar Benin (UBTH), Benin; da kuma Asibitin koyarwa na jami'ar Calabar (UCTH), Calabar.
A bayanan da aka samu, akwai asibitocin akalla hudu a Kudu maso yamma, sai dai babu ko guda da aka ambata daga Arewa maso yamma.
Yi wa mata tiyatar haihuwa kyauta
Ya bayyana cewa kafin ƙarshen shekara, za a ƙara wasu cibiyoyin lafiya na tarayya da manyan asibitocin koyarwa domin ƙara faɗaɗa damar samun tallafi a ƙasar baki ɗaya.

Kara karanta wannan
Sauki ya zo: Tinubu ya sake tausayawa al'umma, zai fara raba kuɗi ga yan Najeriya
Bwala ya tunatar da yadda Tinubu ya amince da a yi wa mata masu juna biyu tiyatar haihuwa (CS) kyauta a asibitocin tarayya, matakin da aka ɗauka don inganta kiwon lafiyar masu juna biyu da rage mace-mace yayin haihuwa.
“A dunkule, waɗannan matakan na nuna yadda ake aiwatar da manufofin Renewed Hope na shugaban kansa, don tabbatar da cewa babu ɗan Najeriya da zai rasa kiwon lafiya saboda rashin kuɗi."
- Daniel Bwala.

Source: Twitter
Martanin wasu masu amfani da X
@IykeEZ2 ya mayar da martani ga Bwala:
“Daniel, taken labarin da da kyau, amma a gaskiya wannan salon farfaganda ne na gwamnatin Najeriya.
"Rage kuɗin wankin koda yana da kyau a rubuce, amma mafi yawan jama’a ba sa samun kulawar lafiya a matakin farko ma, balle su iya ɗaukar nauyin yin wankin ƙoda sau da dama a asibitocin tarayya.
“Haka aka rinka yayata “tiyatar haihuwa kyauta” ga mata masu juna biyu, alhali mata talakawa a karkara na mutuwa kullum saboda matsalolin da za a iya magancewa."
@IAmNotBias ya ce:
“To, kuna tsammanin za mu yi tafi saboda Tinubu “ya rage kudin wankin koda” daga ₦50,000 zuwa ₦12,000? Kar a manta marasa lafiya na buƙatar wanke ƙoda sau 2–3 a mako.
“Wannan na nufin har yanzu talaka zai kashe ₦96,000 zuwa ₦144,000 a wata, a ƙasar da ake biyan mafi ƙarancin albashin ₦70,000. Ta yaya hakan ya zama ‘kiwon lafiya mai sauƙi’?”
Kano: An dakatar da likita kan wankin koda
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kano ta dakatar da wata likita mai wankin koda a asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase (asibitin Nassarawa).
Shugaban hukumar kula da manyan asibitocin Kano, Dr. Mansur Mudi Nagoda ne ya bayyana dakatar da likitar saboda kin zuwa wanke kodar wani mara lafiya.
Ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta samar da dukkanin kayan aiki a asibitocin jihar saboda haka ba za su bari ma'aikata suna wasa da rantsuwar aiki ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
