Yadda wata mata ta yi wa kanta tiyata da reza ta ciro jariri

Yadda wata mata ta yi wa kanta tiyata da reza ta ciro jariri

Wata mace 'yar kasar Tanzania ta yi wa kanta tiyatar haihuwa a gidan ta da ke wani kauyen Kirondo kusa da tafkin Tanganyika a Kudu maso Yammacin kasar.

'Yan sandan kasar sun tabbatar da afkuwar lamarin inda suka bayyana sunan matar Ms Joyce Kalinda 'yar shekara 30 a duniya.

Joyce Kalinda tayi amfani da reza ne wurin yin tiyatar kuma ta ciro jaririn ta.

DUBA WANNAN: Zanga-zanga: Jami'an tsaro sun shiga farautar mabiya Shi'a a Abuja

Ta baro asibitin Kirando ne cikin nakuda sakamakon rashin kulawa da ta ke ganin ma'aikatan jinyan asibitin ba su bata ba kamar yadda jaridar Daily News ta ruwaito.

Ta jima tana neman a taimaka mata na tsawon lokaci amma ba bu wanda ya kula ta inji jardar.

Babban jami'in 'yan sandan yankin ya ce Joyce ta aiki 'yar ta ne, amma 'yar ta dawo ta tarar da mahaifiyarta da jariri, daga nan sai 'yar ta garzaya wurin makwabta domin neman taimako.

An sake mayar da ita asibitin Kirondo inda likitoci suka gudanar da bincike a kanta da jaririn kuma suka tabbatar cewa suna cikin koshin lafiya.

Wannan jaririn shine na takwas da ta haifa kuma na farko da ta haifa ta hanyar tiyata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164