El-Rufai ya kaddamar da na’urorin wankin koda guda 9 don amfanin masu cutar koda a Kaduna

El-Rufai ya kaddamar da na’urorin wankin koda guda 9 don amfanin masu cutar koda a Kaduna

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya kaddamar da wata cibiyar wankin koda dake cikin harabar babban asibitin karamar hukumar Kaduna ta kudu, asibitin tunawa da Yusuf Dantsoho, wanda akafi sani da suna Asibitin Dutse.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito al’ummar unguwar Tudun Wada Kaduna ne suka kikiri wannan cibiya, sa’annan suka samar da dukkanin ayyukan da ake bukata don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu a cibiyar.

KU KARANTA: Na cika alkawarin dana dauka a shekarar 2015 – Buhari ga yan Najeriya

El-Rufai ya kaddamar da na’urorin wankin koda guda 9 don amfanin masu cutar koda a Kaduna
El-Rufai
Asali: Facebook

A jawabinsa, Gwamna El-Rufai ya bayyana jin dadinsa da wannan tsari na jama’an Tudun Wada, sa’annan yayi alkawarin gwamnatin jahar za ta basu duk gudunmuwar da suke bukata don tabbatar da aikin cibiyar yadda ya kamata.

“Gwamnatin jahar Kaduna za ta cigaba da tabbatar da tsarin cibiyar nan ya cigaba, kuma na dauki alkawarin tallafa ma cibiyar da kayan aiki a duk lokacin da bukatar hakan ta tashi, na yaba da kokarin jama’an Tudun Wada, ina fatan Allah Ya saka musu da alheri.” Inji shi.

El-Rufai ya kaddamar da na’urorin wankin koda guda 9 don amfanin masu cutar koda a Kaduna
El-Rufai
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar abokan asibitin Dutse, Alhaji Yusuf Nadabo ya bayyana cewa sun samu nasarar kammala aikin cibitar ne ta hanyar harhada kawunan jama’a, tare da wayar musu da kai akan muhimmancin taimakon kai da kai ba tare da komai sai an jira gwamnati ba.

“Gudunmuwar da Alhaji Mukhtar Monrovia ya bayar na naira miliyan 15, dasu muka sayo na’urorin wankin koda, a yanzu haka an kaddamar da na’urorin wankin koda guda 9, hakan zai baiwa talaka daman samun kulawa a wannan cibiyar.

“Don haka nake kira ga jama’an Tudun Wada dasu daure su cigaba da biyan harajin naira hamsin hamsin a duk sati da muka daura ma kawunanmu don ganin cibiyar bata mutu ba, sa’annan ina kira ga sauran masu kudi da suyi koyi da Monrovia.” Inji Nadabo.

El-Rufai ya kaddamar da na’urorin wankin koda guda 9 don amfanin masu cutar koda a Kaduna
El-Rufai, Balaraba da Monrovia
Asali: Facebook

An sanya ma wannan cibiya sunan Hajiya Amina Ahmad Morovia, mahaifiyar Mukhtar Morovia, wanda ta rasu a sakamakon cutar koda. Daga karshe gwamnan jahar Kaduna ya baiwa cibiyar gudunmuwar naira miliyan daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel