Dikko Radda da Wasu Gwamnoni 6 da Suka Yi Hatsari Suna kan Mulki, 2 daga ciki Sun Rasu

Dikko Radda da Wasu Gwamnoni 6 da Suka Yi Hatsari Suna kan Mulki, 2 daga ciki Sun Rasu

A yayin gudanar da ayyukan gwamnati, gwamnoni a Najeriya sun fuskanci ƙalubale daban-daban, ciki har da haɗurra masu barazana ga rayuwa.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

A daren ranar Lahadi, 20 ga watan Yui, 2025 aka samu labarin cewa gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya gamu da hatsarin mota a Daura.

Gwamnonin da suka taɓa yin hatsari.
Gwamnoni 7 da suka haɗu da jarabawar hatsari lokacin da suna kan mulki a Najeriya Hoto: Alhaji Yahaya Bello, Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Sakataren watsa labaran gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula Muhammed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Wannan al'amari dai ya ja hankalin ƴan Najeriya musamman al'ummar jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku gwamnoni da suka gamu da hatsari a lokacin suna kan mulki a Najeriya.

Wasu daga cikin gwamnonin sun tsira da raunuka, yayin da wasu kuma suka rasa rayukansu.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun koka da tsarin ɗaukar ma'aikatan gwamnati, sun gano matsaloli

1. Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda

Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa na jihar Katsina ya gamu da hatsarin mota a kan titin Daura zuwa Katsina ranar Lahadi.

A sanarwar da gwamnatinsa ta fitar, ta ce mai girma gwamna ya tsira kuma yana cikin ƙoshin lafiya bayan ƙaramin hatsarin da ya rutsa da shi a titin Daura.

"Muna farin cikin tabbatar wa da jama’a cewa Gwamna Radda na cikin koshin lafiya kuma yana cikin yanayi mai kyau, bai ji wani rauni mai tsanani ba." in ji sanarwar.

Bayanai sun nuna cewa hatsarin ya afku ne lokacin da wata mota ƙirar Golf ta kauce hanya, ta buga wa motar da Gwamna Raɗɗa ke ciki a hanyar zuwa Daura.

Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina.
Gwamnan Katsina ya gamu da hatsari a titin Daura zuwa Katsina Hoto: Dr. Dikko Umar Radda
Source: Facebook

Gwamnatin Katsina ta ce Dikko na tare da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, Abdulkadir Mamman Nasir, Hakimin Karaye da Alhaji Shamsu Funtua lokacin da haɗarin ya afku.

Daraktan yaɗa labaran gwamnan Katsina, Maiwada Dammallam ya shaidawa BBC Hausa cewa da farko an kai su asibiti a Daura, daga bisani aka dawo da su Katsina.

Kara karanta wannan

An samu karaya yayin da gwamna Radda da jami'ansa suka yi hadari

"Bayan likitoci sun yi gwaje-gwaje, sun tabbatar da cewa gwamnan na cikin ƙoshin lafiya," in ji shi.

Maiwada ya ce mai girma gwamna ya rage yawan motocin da ke masa rakiya tun bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari saboda yawan zuwa Daura da dawowa Katsina da yake yi.

2. Adams Oshiomhole na Edo (2013)

Gwamna Adams Oshiomhole, ya tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota da ya auku a kauyen Ewu, da ke titin Benin-Auchi a Jihar Edo, a ranar Asabar, 28 ga Disamba, 2013.

Hatsarin ya faru ne lokacin da wata mota Peugeot J5 da ke cike da tumatir da ayaba ta kuɓuce wa direbanta, ta yi karo da motar da gwamna ke ciki.

Tsohon gwamnan Kogi, Adams Oshiomhole.
Sanata Oshiomhole ya haɗu da hatsarin mota a lokacin da yake gwamnan Edo Hoto: Adams Oshiomhole
Source: Facebook

Motoci guda uku da ke cikin ayarin gwamna sun riga sun wuce motar Peugeot J5 kafin motar ta bugi motar da Oshiomhole da dogarinsa (ADC) ke ciki.

Channels tv ta ce motar gwamnan ta lalace sosai, amma babu wanda ya ji rauni a cikin motocin biyu, wacce Oshiomhole ke ciki da Peugeot J5.

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina Dikko Radda ya yi bayani daga asibiti bayan haɗarin mota

3. Rochas Okorocha na Jihar Imo (2013)

A cikin watan Afrilu 2013, Gwamnan jihar Imo na wancan lokacin, Rochas Okorocha ya samu rauni a wani haɗarin mota a cikin birnin Owerri.

Okorocha na kan har zuwa duba wasu ayyuka da gwamnatinsa ke yi a Owerii, ba zato wata mota ƙirar Marsandi ta yi taho mu gama da motar da yake ciki.

Sanata Rochas Okorocha.
Tsohon gwamnan Imo, Okorocha ya taya gamuwa da hatsari lokacin yana mulki Hoto: Rochas Okorocha
Source: Facebook

Likitan gwamnan, Dr Sylvester Igwe ya bayyana cewa Okorocha ya samu ƙaramin rauni a goshi, amma yana cikin ƙoshin lafiya, kamar yadda PM News ta rahoto.

4. Alhaji Yahaya Bello na Kogi (2018)

A watan Afrilu 2018, Gwamna Yahaya Bello ya fado daga motarsa ana tsakiyar tafiya yayin da yake gaisawa da masoyansa, Guardian ta kawo a rahotonta.

A wata sanarwa da gwamnatin Kogi ta fitar, ta ce gwamnan ya samu karaya a ƙafarsa ta hannu da kuma rauni a hannunsa sakamakon haɗarin da ya afku.

Kara karanta wannan

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda ya yi hatsari, an ji halin da yake ciki

Bayanai sun nuna cewa Yahaya Bello, wanda ke cikin motar BMW ya yi yunkurin dora kafarsa ƙofa don jefa kudi a cikin jama’a amma ya zame ya fadi a lokacin da motar ke tafiya.

Sai dai bayan ɗan lokaci, Gwamna Bello ya warke kuma ya ci gaba da aiki har zuwa ƙarshen wa'adinsa na biyu a shekarar 2024.

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello
Yahay Bello ya katya ƙafa a hatsarin da ya yi lokacin yana shugabancin Kogi Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Source: Facebook

5. Idris Wada na Kogi (2013)

The Nation ta ruwaito cewa Gwamnan jihar Kogi, Idris Wada, ya ji rauni a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a watan Disamba, 2012.

Jami’in tsaronsa na musamman (ADC), ASP Idris Mohammed, ya rasu a hatsarin, amma gwamnan ya tsira da munanan raunuka.

An ce tayar motar gwamnan ce ta fashe ne yayin da suke dawowa daga Anyigba, inda ya halarci taron ilimi na kabilar Igala. Hatsarin ya faru ne a kauyen Emi-Woro.

Tsohon gwamnan Kogi, Idris Wada.
Idris Wada na ɗaya daga cikin gwamnonin da suka yi hatsari a kan mulki Hoto: Onugwu Muhammed
Source: Facebook

6. Gwamnan Taraba, Ɗanbaba Suntai a 2012

A ranar 25 Oktoba 2012, Gwamnan Jihar Taraba na wancan lokacin, Danbaba Danfulani Suntai, ya gamu da hadarin jirgi mai saukar ungulu a kusa da filin jirgin saman Yola.

Duk da cewa ya tsira, ya samu munanan raunuka na kwakwalwa da suka hana shi ci gaba da gudanar da mulki har zuwa ƙarshen wa’adinsa, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Daga zuwa taimakon ƴan uwansu musulmi, matasa 4 sun rasu a Kano

Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Suntai ne ya tuƙa jirgin, wanda ke ɗauke da mutane huɗu, duk da ba shi da lasisin tuƙin jirgin sama.

A rahoton da hukumar binciken haɗurra ta ƙasa (AIB) ta fitar, ta tabbatar da cewa Gwamma Suntai ba shi da lasisin tuƙa jirgin sama, wanda hakan ya jawo hatsarin.

Tsohon gwamnan Taraba, Danbaba Suntai.
Gwamnan Taraba, Danbaba Suntai ya yi hatsarin jirgi a lokacin da yake mulki Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Ɗanbaba Suntai ya samu munanan raunuka a hatsarin, kuma ya sha fama da jinya daga wannan asibitin zuwa wancan kafin ya rasu a 2017 a Amurka.

7. Patrick Ibrahim Yakowa na Kaduna (2012)

Gwamnan Jihar Kaduna na baya, Patrick Ibrahim Yakowa, ya rasa ransa a wani mummunan hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a hanyar dawowa daga jana'aiza a Bayelsa.

Marigayi Gwamna Yakowa na tare da mutane biyar a cikin jirgi mai saukar angulo lokacin da hatsarin ya faru a jejin Okoroba, karamar hukumar Nembe ta jihar Bayelsa.

Tsohon gwamnan Kaduna, Patric Ibrahim Yakowa.
Gwamna Yakowa ya rasu a hatsarin jirgin sama a Bayelsa Hoto: @Danee_NK
Source: Facebook

Vanguard ta tattaro cewa waɗanda ke tare da gwamnan sun haɗa da tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Janar Andrew Owoye Azazi.

Sauran sun haɗa da hadimin Azizi, Kamal Mohammed, wani fitaccen ɗan siyasa daga Kaduna, Dauda Psokho da matuƙan jirgi biyu, Mohammed Daba da Lt Col. Adeyemi O. Sowole.

Kara karanta wannan

Ana saura shekara 2 ya sauka, Gwamna Abba ya fadi aikin da ya rage masa a Kano

Dukkan mutane shida da ke cikin jirgin saman mai lamba Navy Agusta NN07, sun mutu a hatsarin wanda ya faru jim kaɗan bayan tashinsa.

Gwamnan Katsina ya yi godiya ga jama'a

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Dikko Tadda ya bayyana cewa ya samu sauƙi bayan hatsarin da ya rutsa da shi a titin Katsina zuwa Daura.

Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Radda na asibitin koyarwa na Katsina, inda ake masa gwaje-gwaje domin tabbatar da lafiyarsa.

Sao dai gwamnan ya fito ya yi godiya ga ɗaukacin al'umma da masoya, waɗanda ke masa addu'o'i da fatan warwarewa tun bayan faruwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262