Magoya Bayan APC 8 Sun Sheka Lahira a Hatsarin Mota, Matawalle ya Dakatar da Kamfen a Zamfara

Magoya Bayan APC 8 Sun Sheka Lahira a Hatsarin Mota, Matawalle ya Dakatar da Kamfen a Zamfara

  • Magoya bayan jam'iyyar APC takwas ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota da suka tafka yayin dawowa daga kamfen a jihar Zamfara
  • Lamarin ya faru ne bayan mota uku sun yi gamon kashe mu raba da juna a babbar hanyar Gummi zuwa Bukkuyum ta jihar Zamfara
  • Gwamna Bello Matawalle ya dakatar da kamfen dinsa a Bukkuyum domin makokin wadanda suka rasu sannan ya je har garin an yi jana'iza da shi

Zamfara - A kalla magoya bayan jam'iyyar APC mai mulki takwas ne suka kwanta dama a jihar Zamfara sakamakon mummuna hatsarin mota da suka tafka a kan babbar hanyar karamar hukumar Gummi zuwa Bukkuyum a jihar.

APC Zamfara
Magoya Bayan APC 8 Sun Sheka Lahira a Hatsarin Mota, Matawalle ya Dakatar da Kamfen a Zamfara. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Lamarin ya faru a daren Alhamis yayin da magoya bayan Gwamna Bello Matawalle na jihar da ke dawowa daga kamfen din APC a Gummi suka tafka hatsari da motoci uku wanda a take mutum takwas suka mutu.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Bindige Kansila Har Lahira A Jihar Arewa

Hadimin Gwamna Matawalle na bangaren yada labarai, Zailani Bappa, ya bayyana hakan ne a takardar da ya faitar ranar Juma'a, Channels TV ta rahoto.

Matawalle ya dakatar da kamfen

Yace lamarin yasa Ubangidansa ya dakatar da kamfen dinsa a karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara domin makokin mamatan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Gwamna Bello Mohammed, Matawallen Maradun, ya dakatar da kamfen dinsa a karamar hukumar Bukkuyum domin makokin mutum takwas wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin mota kan babbar hanyar Gummi zuwa Bukkuyum a daren jiya."

- Takardar tace.

"Lamarin ya faru ne bayan sallar Magrib yayin da motoci uku suka yi gamon kashe mu raba inda suka halaka mutum shida har da masu sabon aure.
"Biyar daga cikin gawawwakin an sallacesu bayan sallar Juma'a a Bukkuyum da rana inda gwamnan da tawagarsa suka halarta."

Kara karanta wannan

Rai Bakon Duniya: Mummunan Hatsari Ya Rutsa da Jiga-Jigan Jam'iyar APC Mai Mulki

- Ya kara da cewa.

Gwamna yayi wa Sarki ta'aziyya

Gwamnan ya karasa har zuwa fadar Sarkin Bukkuyum, Alhaji Mohammed Usman inda ya je ya mika ta'aziyya ga iyalansa da jama'ar Bukkuyum baki daya.

Ya kwatanta lamarin da kaddarar Allah inda yayi fatan gafarar Ubangiji ga mamatan.

Kamar yadda mai magana da yawun gwamnan ya bayyana, Matawalle yayi umarni ga mataimakin Gwamnan jihar, Ibrahim Wwakkala Liman da yayi addu'a ta musamman ga wadanda suka rasu a fadar.

Tagwayen bam sun tashi a wurin kafen din APC a Ribas

A wani labari na daban, wasu abu masu fashewa guda biyu sun tashi da jama'a ana tsaka da kamfen din APC a Fatakwal da ke jihar Ribas.

An tattro yadda mutum uku suka matukar jigata sakamakon lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel