Muhimman darussa abin lura daga rayuwar marigayi Dan Baba Suntai
- A jiya Laraba ne aka bayyana mutuwar tsohon gwamnan Taraba Dan Baba Suntai
- Suntai ya rasu ne sakamakon jinya da yayi bayan hadarin jirgin sama
A ranar 25 ga watan Oktoban shekara 2012 ne marigayi tsohon gwamnan jihar Taraba, Danbaba Suntai ya samu hatsarin jirgin sama yayin dayake kokarin saukar da jirgin nasa wanda yake tukawa da kansa.
Shi dai Dan Baba an haife shi ne a ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 1961 a karamar hukumar Bali na jihar Taraba, inda ya halarci makarantar Kwalejin gwamnatin tarayya ta Kano da kuma jami’ar Ahmadu Bello.
KU KARANTA: Miji da mata sun taka sawun ɓarawo: An kama su da wayar wata mata da aka yi garkuwa da ita, kuma aka kashe ta
Abinka da kaddara, tun bayan da gwamnan ya gamu da hatsarin, sai ya zama abin tausayi, sai dai a daga a kwantar, baya iya magana, baya iya gane mutane. Ikon Allah! Idan yau kaine, gobe ba kai bane.
A lokacin da hatsarin jirgin saman ya rutsa da gwamna Suntai, babu wanda ya fi shi iko a jihar Taraba, shike da iko da kowa da komai a jihar Taraba, duba da ikon da kundin tsarin mulki ya bashi, amma kash, gwamnan bashi da iko da jirgin sama, karfen nasara, kuma bashi da iko da kaddara.
Idan da dukiya nasa mutum ya tsira daga kaddara ko mutuwa, tabbasa da Dan baba bai shiga wannan mummunar hadari ba, kai ma bai mutu ba a yanzu. Haka nan idan da kudi na siyan lafiya, da yanzu shine gwamnan jihar Taraba, ko kuma ya sauka, amma yana majalisar dattawa kamar yadda abokansa suke.
Kaico, Dan Baba bashi da ikon yin daya daga cikin wadannan abubuwan da muka ambata, babu wani mahaluki dake wannan dama sai Ubangiji Allah. Amma abin mamaki shine har yanzu mutane basa duakan darasi daga mutuwa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Najeriya kasa daya?
Asali: Legit.ng