A daina danganta mutuwar Yakowa da Isa Pantami, Musulmai inji Shugaban kungiyar CAN

A daina danganta mutuwar Yakowa da Isa Pantami, Musulmai inji Shugaban kungiyar CAN

- John Hayab ya yi magana a kan zargin Musulmai da kisan Patrick Yakowa

- Shugaban kungiyar na CAN ya ce a daina zargin Isa Pantami ko JNI da laifi

- Malamin addinin ya musanta jita-jitar da wasu ke yadawa a kafafen zamani

Shugaban kungiyar CAN ta jihar Kaduna, John Joseph Hayab, ya yi watsi da zargin da ake yi wa Isa Ali Pantami na hannu a mutuwar Patrick Yakowa.

John Joseph Hayab, wanda ya rike mukamin mai ba Marigayi tsohon gwamnan Kaduna, Patrick Yakowa, shawara kan harkar addini, ya karyata rade-radin.

Da yake magana a wani jawabi da ya fitar a ranar Alhamis, John Hayab ya ce bai kamata a yarda da wannan jita-jitar ba, har sai an yi cikakken bincike.

KU KARANTA: Pantami: Dalilin da ya sa Majalisa ta ki tattaunawa a kan Minista

Ya ce: “Yadda abubuwa su ka juya su na tada mani hankali, musamman lamarin alakanta Isa Pantami da musulmai da mutuwar Patrick Ibrahim Yakowa.”

Malamin addinin yake cewa an dogara ne da wasu takardu da akwai alamar tambaya a game da ingancinsu. Jaridar The Cable ta fitar da wannan rahoto.

“Coci da dangin Yakowa su na ganin nauyin wannan zargi, tare da yiwuwar hakan ya iya jawo matsala wajen zaman lafiya da sha’anin tsaro na kasa.”

“Haka zalika, coci na da ta-cewa game da wasu bayanai, kamar wanda Pantami yayi a baya, wanda yanzu haka ake yawo da su a dandalin sadarwa.” Inji shi.

KU KARANTA: Buhari ne babban maƙiyin Najeriya - Shugaban Afenifere

Jagoran na kungiyar kiristocin Najeriya ya ce sabani da mutum ba dalili ba ne da za a amince da duk wani sharri da ake nemansa da shi a wannan zamani.

Hayab ya ce akwai bukatar a binciki takardar nan da ake cewa daga kungiyar JNI na reshen jihar Bauchi ta fito, ba a rika yawo da shi a kafafen sadarwa ba.

A cewar John Hayab, ba a yi bincike bayan mutuwar Patrick Yakowa ba, abin da kurum aka sani shi ne jirgin saman da yake ciki ne ya samu matsala a ranar.

A jiya fadar shugaban kasar Najeriya ta mayar da martani game da zargin cewa Dr. Isa Pantami, ya yi wasu kalamai a baya yana goyon bayan 'yan ta'adda.

A halin yanzu, Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani na kasa, Isa Pantami, ya na shan suka kan maganganun da yayi wadanda ke cike da rudani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel