Gwamnatin Kogi Ta Fadi Gaskiya Kan Zargin Karkatar da N100bn da EFCC Ke Yi Wa Yahaya Bello

Gwamnatin Kogi Ta Fadi Gaskiya Kan Zargin Karkatar da N100bn da EFCC Ke Yi Wa Yahaya Bello

  • Gwamnatin jihar Kogi ta fito ta kare tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, kan tuhumar da hukumar EFCC ke yi masa
  • A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar ya fitar, ya zargi hukumar da ƙoƙarin ɓata sunan tsohon gwamnan
  • Gwamnatin ta haƙiƙance cewa kuɗaɗen jihar basu ɓace inda ta yi nuni da cewa wasu ƴan siyasa ke amfani da hukumar don ganin bayan Bello

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta soki hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC), kan tuhumar tsohon gwamnan jihar Yahaya Bello.

Gwamnatin ta bayyana zargin cin hanci da rashawan a matsayin ƙagaggen zance da nufin taɓa ƙimar tsohon gwamnan, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar PDP, bayanai sun fito

Gwamnatin Kogi ta kare Yahaya Bello
Gwamnatin Kogi ta zargi EFCC da kokarin bata sunan Yahaya Bello Hoto: Yahaya Bello
Asali: Facebook

Hukumar EFCC, a cikin tuhumar da ta yi wa shugaban ma’aikatan fadar gwamnati mai ci, Alli Bello, ta tuhumi Yahaya Bello da laifin karkatar da N100bn kafin ya hau kujerar gwamna a watan Satumban 2015.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnayin Kogi ta kare Yahaya Bello

Sai dai kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kingsley Fanwo, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya dage kan cewa kuɗaɗen jihar ba su ɓace ba, kuma ya zargi hukumar EFCC da wata manufa ta siyasa domin ɓata sunan Bello, rahoton gidsn talabijin na Channels tv ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"A matsayinmu na gwamnati, mun gaji manufofin rashin yin sako-sako ga cin hanci da rashawa daga tsohuwar gwamnatin Gwamna Yahaya Bello.
"Muna so mu bayyana cewa kuɗaɗen Kogi ba su ɓace ba, kuma EFCC na ƙoƙarin gano abin da bai ɓace ba. Don haka muna kira ga hukumar EFCC da ta daina ambaton sunan jihar Kogi a ci gaba da muzgunawar da ta ke yi, wacce wasu ƴan siyasa a fadar shugaban ƙasa suka shirya domin ɓata sunan Bello."

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya fadi kuskuren da gwamnati ke yi wajen ceto daliban da aka sace a Kaduna

Fanwo ya kuma yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya bayar da umarnin gudanar da bincike na musamman kan abubuwan da ke faruwa a jihar don hana wasu ƴan siyasa yin amfani da hukumar EFCC a matsayin karan farauta.

KIDA ta goyi bayan Yahaya Bello

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƴan jihar Kogi mazauna ƙasashen waje (KIDA), ta ɗauki mataki kan hukumar EFCC bisa tuhumar Yahaya Bello.

Ƙungiyar ta buƙaci ƙungiyoyi daban-daban na ƙasa da ƙasa da shiga cikin lamatin don kawo ƙarshen abin da ta kira ƙoƙarin ɓata sunan tsohon gwamnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel