Okorocha: Na yi gwamna ban samu komai ban da karin talauci, sanata bayyana halin da yake ciki

Okorocha: Na yi gwamna ban samu komai ban da karin talauci, sanata bayyana halin da yake ciki

  • Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana cewa kasancewarsa gwamna ya sa ya kara talaucewa ne
  • Okorocha ya ce da kudinsa tun kafin ya hau kujerar gwamna, inda yace yana daya daga cikin yan Najeriya da Allah ya wadata
  • Sanatan mai wakiltan Imo ta yamma a majalisa a yanzu, ya ce yana bin gwamnatin jihar Imo bashin kudi har naira biliyan 8 na tsaro

Mai aniyar zama shugaban kasa kuma jigon jam'iyyar Progressives Congress (APC), Rochas Okorocha, ya ce kasancewarsa gwamnan jihar Imo bai kara masa komai ba sai talauci.

Tsohon gwamnan, wanda ya kasance sanata mai wakiltan Imo ta yamma a yanzu haka, ya ce yana bin gwamnatin jihar bashin naira biliyan 8 na tsaro.

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 31 ga watan Janairu, yayin da ya bayyana a shirin Channels TV na Politics Today wanda Punch ta sanya ido.

Kara karanta wannan

Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi

Okorocha: Na yi gwamna ban samu komai ban da karin talauci, sanata bayyana halin da yake ciki
Okorocha: Na yi gwamna ban samu komai ban da karin talauci, sanata bayyana halin da yake ciki Hoto: PM News
Asali: Twitter

Okorocha, wanda ya kasance gwamnan jihar Imo daga 2011 zuwa 2019, ya kuma bayyana sabon zargin almundahana da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ke masa a matsayin siyasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Punch ta rahoto cewa a ranar Litinin hukumar yaki da rashawar ta tuhumi tsohon gwamnan kan badakalar naira biliyan 2.9 a gaban kotun tarayya, Abuja, yan awanni bayan ya ayyana aniyarsa ta yin takarar shugaban kasa a 2023.

Sai dai ya Okorocha ya karyata zargin inda ya bayyana shi a matsayin kanzon kurege.

Ya ce:

“Wadanda ke cewa na talauce karya suke yi, karya ce suka shirya. Idan ka yi maganar ’yan Najeriya da Allah Ya wadata su, zan daga hannu.
"Na fi kudi kafin na zama gwamna, a zahirin gaskiya, kasancewana gwamna ya sa na kara talaucewa. Kafin na zama gwamna, dukiyata a Abuja kawai, na tabbata za ka iya kirga mutum daya, mutum biyu da za su iya dogara da shi.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

"Nawa ne kudin gwamnatin jihar Imo? Ina bin jihar Imo kudi saboda ban taba karbar kudin tsarona ba, abun da ya kamata na karba daga jihar Imo a yanzu naira biliyan 8 idan har zan bibiyi kudin tsaron da ban karba ba."

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa dai ta sha kai Okorocha gaban kotu bisa zargin almundahana da wasu kadarorinsa da na iyalansa da gwamnatin magajinsa, Hope Uzodinma ta karbe, amma Okorocha ya ci gaba da karyata zargin.

Duk da ya jarraba sa’a sau 3 babu nasara, Sanatan APC zai sake neman Shugaban kasa

A gefe guda, mun ji cewa akwai yiwuwar Sanatan na Imo ta yamma ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023.

Wata kungiya da ke goyon bayan Rochas Okorocha ya nemi kujerar shugaban kasa, New Nigeria Movement (NNM) ta kyankyasa wannan a makon da ya wuce.

Daya daga cikin jagororin tafiyar New Nigeria Movement, Farfesa Aliyu Abdullahi Jibia ya ce Okorocha zai yi wa Duniya jawabi a ranar 31 ga watan Junairu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sanata ya sanar da kudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel