Ana Maganar 2027, 83% na 'Yan Najeriya Sun Nuna Rashin Gamsuwa da Tinubu
- Wani sabon bincike ya nuna cewa kashi 83 na 'yan Najeriya ba su da kwarin gwiwa ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- Binciken ya kuma bayyana cewa kashi 79 na ƴan Najeriya ba su samu gamsuwa ga tsarin shari'a a ƙasar ba
- Rahoton ya bayyana cewa matsin tattalin arziki da hauhawar farashi na daga cikin manyan dalilan da ke haddasa rashin gamsuwar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sabon rahoton da cibiyar API ta fitar ya bayyana cewa yawan 'yan Najeriya na kara rasa kwarin gwiwa ga gwamnati da hukumomin a karkashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu.
Rahoton ya nuna cewa mafi yawan al’umma na nuna fushi da gazawar gwamnati wajen inganta rayuwar jama’a da kare amana.

Source: Facebook
Rahoton jaridar the Guardian ya nuna cewa kaso mafi tsoka na 'yan Najeriya ba su da gamsuwa kan yadda lamuran dokoki ke tafiya a kasar.

Kara karanta wannan
'Zuwansa alheri ne': Ribadu ya faɗi yadda Tinubu ya ceto Najeriya daga tarwatsewa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayani kan rashin gamsuwa da Tinubu
Binciken ya nuna cewa kashi 83 na 'yan Najeriya ba su da kwarin gwiwa ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Haka zalika, kashi 82 sun bayyana rashin gamsuwa ga majalisar kasa da ke karkashin Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas.
Kashi 79 daga cikin wadanda aka tattauna da su sun ce ba su da yarda da bangaren shari’a, wanda yanzu ke karkashin shugabancin alkalin alkalai, Kudirat Kekere-Ekun.

Source: Twitter
Rahoton ya ce wannan yanayi na nuna cewa halin da ake ciki ya fi muni idan aka kwatanta da rahotannin da aka fitar a shekarun 2019, 2021 da 2022.
Matsin rayuwa na kara haɗa kan jama'a
Rahoton ya ce a yanzu 'yan Najeriya sun fara samun hadin kai ta hanyar shan wahalhalun rayuwa, musamman matsin tattali, hauhawar farashi da karancin arziki a gwamnatin Tinubu.
Binciken ya nuna cewa da dama daga cikin al’umma sun ce halin kuncin rayuwa, karancin hanyoyin sufuri da tashin farashin kayan masarufi sun hana su kwanciyar hankali da cigaba.
Yadda ka yi biniken a fadin Najeriya
Punch ta wallafa cewa rahoton ya samo asali ne daga gagarumin binciken da aka gudanar tsakanin watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2025, da goyon bayan gidauniyar Ford.
Jimillar mutane 5,465 aka yi wa tambayoyi ta hanyar ziyartar gidajensu kai tsaye domin tabbatar da daidaito daga kowanne yanki na kasar.
Rahoton ya ce an gudanar da tambayoyin ga mutane da harshen Turanci, Pidgin, Hausa, Igbo da Yarbanci.
Daga cikin muhimman abubuwan da rahoton ya bayyana, akwai cewa kashi 53% na 'yan Najeriya sun ce suna jin takaici da rayuwarsu a Najeriya.
Rarara ya ce Bola Tinubu yana kokari
A wani rahoton, kun ji cewa mawakin jam'iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara ya ce shugaba Bola Tinubu yana kokarin farfado da Najeriya.
Rarara ya ce ba neman tara kudi ko abin duniya ba ne ya sanya shugaban kasar neman kujerar shugabanci a kasar nan.
Mawakin ya ce wasu matsalolin an gaje su ne daga gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sauka a 2023.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
