Asiri Ya Tonu: An Kama Wanda ke Tare Hanya domin Kashe Matafiya a Filato

Asiri Ya Tonu: An Kama Wanda ke Tare Hanya domin Kashe Matafiya a Filato

  • Dakarun rundunar soji sun kama wani mutum da ake zargi da shiga kungiyar ta’addanci a ƙaramar hukumar Barkin Ladi
  • Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun cafke shi a lokacin da ya buya don kai hari, tare da kwato bindiga kirar AK-47 da harsasai
  • Bayanai sun nuna cewa mutumin na shirin kai hari ga matafiya ne da ba su ji ba ba su gani ba a hanyar Kafi Abu-Rakwok

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Dakarun rundunar Operation Lafiyar Jama’a sun damke wani da ake zargi da shiga kungiyar ta’addanci tare da kwato bindiga da harsasai a yankin Barkin Ladi da ke jihar Filato.

Rahotanni daga majiya mai tushe sun bayyana cewa an kama wanda ake zargin mai suna Stephen Gyang, dan shekara 40, ne da misalin karfe 9:12 na dare, ranar Asabar, 6 ga Yuli, 2025.

Kara karanta wannan

Rigiji gabji: Dan Najeriya ya sace miliyoyin bikin rantsar da Donald Trump

Wanda aka kama yana shirin kai hari kan matafiya a Filato
Wanda aka kama yana shirin kai hari kan matafiya a Filato. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa sojojin sun ce an kama shi ne bayan samun sahihin bayanan sirri da suka nuna cewa yana shirin kai hari ga matafiya a hanyar Kafi Abu-Rakwok.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda aka kama da shirin kai hari a Filato

Bayanan sirri sun bayyana cewa Stephen Gyang ya buya ne a gefen hanya, inda ya shirya kai hari ga mutanen da ke wucewa ba tare da sanin komai ba.

Dakarun da ke gudanar da aikin sintiri a yankin sun yi gaggawar mamaye wurin, inda suka kama wanda ake zargin ba tare da wata matsala ba.

Binciken farko ya nuna cewa an samu bindiga kirar AK-47 hadin gida mai cike da harsasai guda 30 daga hannun Stephen Gyang.

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang. Hoto: Plateau State Government
Source: Facebook

An mika shi don bincike da daukar mataki

Wanda ake zargin ya fito ne daga kauyen Kafi Abu, wanda ke cikin ƙaramar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon minista a Filato, sun yi kisa

Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka yana hannun jami’an tsaro domin ci gaba da bincike da kuma matakin doka da ya dace.

Ana ganin kama wannan mutum wata babbar nasara ce wajen hana hare-haren da ake yawan fuskanta a sassan jihar Filato.

Matafiya na fama da hare-hare a Filato

Hanyar Kafi Abu-Rakwok da ke cikin jihar Filato na daya daga cikin hanyoyin da ake fama da hare-haren ta’addanci, inda matafiya da dama suka rasa rayukansu a lokuta daban-daban.

Hukumomi sun yi alkawarin ci gaba da kai daukin gaggawa da kara yawan sintiri domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin.

Maganar Uba Sani kan kisan matafiya a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya koka kan yadda aka kashe wasu matafiya da suka je wucewa a jihar Filato.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe matafiyan ne da suka fito daga Zariya, jihar Kaduna yayin da suka tsaya za su yi tambaya a kan hanya.

Gwamnan ya yi Allah wadai da kisan yana mai cewa dole a tabbatar an dauki matakin da ya dace kan wandanda suka yi kisan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng