An Shiga Tashin Hankali a Katsina, Ƴan Bindiga Sun 'Ƙwace Ikon' Karamar Hukuma

An Shiga Tashin Hankali a Katsina, Ƴan Bindiga Sun 'Ƙwace Ikon' Karamar Hukuma

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga karkashin jagorancin Babaro sun kwace ikon ƙaramar hukuma a Katsina
  • An kashe mutane da dama, wasu kuma an sace su lamarin ya jefa al'umma cikin halin tsoro da rudani
  • Mazauna yankin sun roƙi Gwamna Dikko Radda da gwamnatin tarayya da su ɗauki matakin gaggawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kankara, Katsina - Al'ummar jihar Katsina sun shiga tashin hankali bayan mamayar yan bindiga a yankuna da dama.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa miyagun sun kwace iko a karamar hukumar Kankara da ke jihar.

Ana fargabar yan bindiga sun karbe ikon wata karamar hukuma
Ana yada jita-jita cewa yan bindiga sun karbe ikon karamar hukuma a Katsina. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton Bakatsine, wanda ke kawo rahotanni kan tsaro ya tabbatar da labarin a shafin X a yau Alhamis 26 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka taba cafke Babaro a Katsina

Hatsabibin dan bindiga, Babaro na daga cikin miyagu da suka addabi jihar Katsina musamman yankin karamar hukumar Kankara.

Kara karanta wannan

Matashi ya hau kan dogon ƙarfe a Kano, ya buƙaci wasu fitattun mutane su je wurin

Ko a watan Afrilun 2024 ma, jami'an tsaron hadin gwiwa sun yi nasarar cafke Babaro sai dai daga bisani an sake shi.

Bayan sakin nasa, mutane da dama sun yi ta korafi kan dalilin haka wanda har suke zargin hukumomi da daurewa yan ta'adda gindi.

Sanarwar Bakatsine ta ce:

"Ƴan bindiga ƙarƙashin jagorancin ɗan ta'adda Babaro sun karɓe ikon Karamar Hukumar Kankara a Jihar Katsina.
"An haramta noma daga Marabar Kankara har zuwa Yantumaki, inda aka kashe da sace mutane da dama. Harkar kiwon lafiya ta durƙushe gaba ɗaya.
"Mazauna yankin suna roƙon Gwamna Dikko Umaru Radda da Gwamnatin Tarayya da su kawo ɗaukin gaggawa kafin lamarin ya ke ƙara tabarbarewa."

Kankara na shan fama da yan bindiga

Karamar Hukumar Kankara na daga cikin wuraren da ke fama da rikice-rikice da sace-sacen mutane akai-akai, a watan Disambar 2020 aka sace ɗaliban makaranta fiye da 300, lamarin da ya tayar da ƙura a fadin ƙasa.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, Gwamnatin Jihar Katsina da kuma hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba kan wannan lamari.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace amarya awa 2 kafin ɗaurin aurenta, sun bindige yayanta

Wasu yan bindiga sun mamaye karamar hukuma a Katsina
Ana fargabar yan bindiga sun karɓe ikon ƙaramar hukuma a Katsina. Hoto: Dikko Umaru Radda.
Source: Facebook

Yadda yan bindiga suka hana noma a Katsina

Majiyoyi suka ce yan bindiga ƙarƙashin hatsabibi, Babaro sun kwace ikon Karamar Hukumar gaba daya.

An ce bayan karbe ikon, sun kuma kafa doka da oda musamman ga al'ummar yankin, kamar yadda rahoton Leadership ya ce.

Miyagun sun haramta noma gaba ɗaya daga yankin Marabar Kankara har zuwa Yantumaki wanda ya jefa manoma cikin tsananin tsoro da fargaba.

“Ƴan bindigar na kashe mutane da dama sannan suna sace wasu, an kasa zuwa asibiti saboda barazanar harin ƴan bindiga, harkar lafiya ta durƙushe baki ɗaya.”

- Cewar wani da ya buƙaci a ɓoye sunansa

Mazauna Kankara sun roƙi Gwamna Dikko Umaru Radda da gwamnatin tarayya da su ɗauki matakin gaggawa domin kare rayukan jama’a.

Yan bindiga sun yi ta'asa a jihar Katsina

A baya, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari kan manoman yayin da suke ƙoƙarin share gonakinsu a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta tasa ƙeyar ɗan TikTok da ke shigar ƴan daudu zuwa gidan kaso

Miyagun ƴan bindigan sun farmaki manoman ne a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina

Sai dai an ce dakarun sojojin da sauran jami'an tsaro sun kai ɗaukin gaggawa bayan samun rahoton harin da ƴan bindigan suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.