Hadimin Ganduje Ya Caccaki Gwamna, Yana So a Dauki Mataki kan Hatsaniyar Gombe
- Oliver Okpala, hadimin Shugaban APC na kasa ya yi tir da yunkurin kai wa Abdullahi Ganduje hari a Gombe
- Ya bayyana hargitsin da ya afku a matsayin abin kunya kuma babbar barazana ga dimokuraɗiyya a Najeriya
- Ya gode wa ‘yan sanda da jami’an tsaro da suka dakile rikicin, yana mai cewa siyasa ba ta tashin hankali ba bace
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Oliver Okpala, mai ba shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, shawara kan wayar da kai, ya ya yi kaca-kaca da yadda aka tayar da tarzomar a taron jam'iyya a Gombe.
A taron APC na shiyyar Arewa maso Gabas da ya gudana a ranar Lahadi, an tashi taro a cikin hayaniya, yayin da jami'an tsaro suka gaggauta raka Ganduje motarsa.

Source: Facebook
The Cable ta ruwaito cewa Okpala ya bayyana yunkurin da wasu suka yi na kai hari kai tsaye kan Ganduje a yayin taron a matsayin rashin kishin ƙasa, da abin kunya.
Hadimin Abdullahi Ganduje ya fusata
Jaridar Punch ta wallafa cewa Ganduje ya gargaɗi cewa irin wannan ɗabi’a ta tashin hankali kamar yadda aka gani a Gombe bai dace da tsarin dimokuraɗiyya ba.
Oliver Okpala ya ce:
“Yunkurin da wasu mutane suka yi na kai hari ga shugaban jam’iyya yayin da yake kusa da motarsa abin takaici ne.”
“Muna godiya ga ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da suka shiga tsakani cikin gaggawa. Da ba su dauki mataki ba, lamarin na iya rikidewa ya zama hargitsi sosai”
Okpala ya jaddada cewa faruwar irin wannan al’amari a gaban gwamnoni da jagororin jam’iyya lamari ne mai hatsari kuma ba za a ƙyale shi ya wuce haka nan ba.

Kara karanta wannan
Bayan ya sha da kyar, shugaba a APC ya kara kinkimo faɗa kan batun cire Shettima a 2027

Source: Facebook
Ya ce:
“Babu gurbin ‘yan daba a siyasar Najeriya ta yanzu. Siyasa ta tattaunawa ce, ba ta tashin hankali ba."
Okpala ya yaba da irin jajircewar Ganduje
Okpala ya nuna cewa Ganduje na kokari ba dare ba rana wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a jam’iyyar da kuma faɗin ƙasar baki ɗaya.
A cewarsa:
“Dr. Ganduje ya nuna hazaka a shugabanci, yana aiki ba kakkautawa don haɗa kan ‘ya’yan jam’iyya, kuma yana da kyakkyawar mu’amala da shugaban ƙasa da mataimakinsa.”
“Abin takaici, wasu kalilan daga cikin mahalarta taron sun ki jin kiran zaman lafiya da tuntuba da ya yi, suka nace sai sun tayar da hankali.”
An taso Zulum a gaba kan hayaniyar APC
A baya, mun ruwaito cewa kungiyar APC ta yankin Arewa ta Tsakiya ta nuna fushinta kan tarzomar da ta auku a Gombe a taron jam'iyya ta ranar Lahadi, 15 ga Yuni, 2025.
Shugaban kungiyar, Saleh Zazzaga, ya zargi Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, da daukar ‘yan daba da nufin kai hari ga Ganduje a wajen taron yankin Arewa maso Gabas.
Kungiyar ta bukaci Gwamna Zulum da ya fito ya nemi afuwa kan abin da ya faru, tana mai cewa wannan abu ya sabawa tsarin daidaito da girmama juna a cikin jam’iyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

