'An Yi ne saboda Fubara': Shugaban Riko Ya Faɗi Abin da Ke cikin Kasafin Kuɗin Rivers
- Shugaban mulkin riko na jihar Rivers, Ibok-Ete Ibas ya bayyana cewa kasafin 2025 yana sa ran dawowar Gwamna Siminalayi Fubara
- Admiral Ibas mai ritaya ya ce an tsara kasafin ne daidai da tsarin ci gaba na jihar, inda aka ware kudi don gine-gine, ilimi, da lafiyar al’umma
- Shugaban kwamitin majalisa, Julius Ihonvbere, ya sha alwashin duba kasafin sosai tare da hada kai don dawo da zaman lafiya da ci gaba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Shugaban riko na jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya ya yi karin haske kan kasafin kudi.
Ibas ya ce kasafin N1.48tn na 2025 yana sa ran dawowar Gwamna Siminalayi Fubara da sauran jami’an siyasa da aka dakatar.

Source: Twitter
Ana hasashen dawowar Fubara mulkin Rivers
Ibas ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Laraba, yayin da yake kare kasafin kudin a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, kasafin ya yi daidai da burin tsarin cigaban jihar Rivers na 2017 zuwa 2027 da aka tsara tun da farko don bunkasa jihar.
Ya ce kasafin yana dauke da tsari don tara kudin shiga, bunkasa ababen more rayuwa, ci gaban jari kan mutane da inganta tattalin arziki gaba daya.
Ya ce:
“Saboda jiran dawo da tsarin doka, wannan kasafi ya tanadi kudin ofisoshi na wadanda aka dakatar domin su dawo bakin aiki daga baya.”
Zarge-zargen da Ibok-Ete Ibas ke yi a Rivers
Sai dai, ya zargi wasu jami’an jihar Rivers da kin bayar da muhimman bayanai da za su taimaka wajen tsara kasafin yadda ya kamata.
Ibas ya ce:
“Abin takaici, wasu jami’an gwamnati sun boye muhimman bayanai da suka wajaba a hada su cikin wannan kasafi kafin a mikawa Majalisa.
“Amma saboda halin gaggawa da kuma kare gaskiyar kudin gwamnati, an hada duk bayanan kudi da aka samu a farkon rabin shekara.
Jimillar kasafin ya kai N1.48tn, yayin da ake sa ran tara N1.4tn, kuma an tura kasafin zuwa Majalisa bayan amincewar shugaban kasa da hukuncin kotu.
A jawabinsa, Ibas ya gode wa kwamitin saboda sadaukar da kai, yana mai cewa sun nuna kishin kasa duk da cinkoson aikinsu a Majalisar.

Source: Twitter
Abin da ke cikin kasafin kuɗin Rivers
Ibok-Ete Ibas ya bayyana muhimman kudade da aka ware, ciki har da N324.5bn don ababen more rayuwa da sufuri da kuma N55bn domin fadada asibitin koyarwa.
Sauran sun hada da N50bn don gyaran asibitoci na yankuna, N38.85bn don kiyaye gabar ruwa da kuma N30bn don gyaran makarantun sakandire, Vanguard ta ruwaito.
An ware N5.75bn don gyaran makarantun firamare, N2.5bn don karfafa mata da kuma N3bn don cibiyoyin bunkasa matasa a fadin jihar.
An kuma ware N20bn don habaka bankin 'Microfinance' na jihar da N117bn don fansho, hakkokin ritaya da sauran kudin ma’aikata.
Jonathan na nemawa Fubara afuwa wurin Tinubu
Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan na matsa wa Bola Tinubu lamba don dawo da Gwamna Sim Fubara kafin ranar dimokuradiyya.

Kara karanta wannan
'Ina Katsina, Zamfara?: An taso malaman addini a gaba kan kiran dokar ta ɓaci a Benue
Majiyoyi sun ce Jonathan ne ya jagoranci ganawar sirri da Tinubu tare da umartar Fubara ya kai masa ziyarce-ziyarce.
Ana sa ran Tinubu zai yi jawabi a ranar dimokuradiyya, yayin da ake fatan zai sassauta hukuncin dakatar da Fubara da mukarrabansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

