An Kashe Direbobi Hausawa a Imo, An Kone Gawarsu a cikin Motar da Suka Dauko Kaya
- Wasu ƴan bindiga sun kashe direbobi biyu tare da kona tirela a jihar Imo, kamar yadda hukumar NURTW ta tabbatar da lamarin
- NURTW ta zargi ƴan IPOB da kai harin, aka ce sun tare hanya tare da buɗe wuta kan direbobin, sannan suka kone gawarsu da motar
- Hon. Balarabe Danja ya yi kira ga kungiyar gwamnonin Arewa da ta dauki mataki kan irin asarar rayukan 'yan Arewa da ake yi a Kudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Imo - Wasu ƴan bindiga sun kashe direbobi biyu tare da kona babbar motarsu kirar tirela a sha-tale-talen Ogi da ke karamar hukumar Okigwe a jihar Imo.
Wannan lamari ya faru ne da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Asabar, kamar yadda jami'an kungiyar direbobi ta kasa (NURTW) reshen Imo suka bayyana.

Kara karanta wannan
Amurka: Wani ɗauke da bindiga ya harbe yar majalisa har lahira, Sanata ya ji rauni

Source: UGC
An kashe direbobi, an kona gawarsu
Shugaban NURTW na Okigwe, Dahiru Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust, inda ya ce sun sanar da jami'an tsaro, ciki har da DPO na Okigwe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake bayar da labarin abin da ya faru, shugaban ya ce:
"Muna zargin ƴan IPOB (masu rajin kafa kasar Biafra) ne suka tare hanyar suka buɗe musu wuta a ranar Asabar. Sun kona motar, wacce ke cike da gari, da kuma gawarwakin."
Dahiru Musa ya ce ya yi gaggawar kai rahoto ga jami'an tsaro, ciki har da sojoji da ƴan sanda a lokacin da lamarin ya faru.
"Sojoji da DPO na Okigwe sun ziyarci wurin da abin ya faru. Ni da ƴan sanda mun kwashe gawarwakin zuwa asibiti, kuma a ranar Litinin, mun yi musu Sallah, mun birne su."
- Dahiru Musa.
Halin da direbobi ke shiga a jihar Imo

Kara karanta wannan
Benue: yan bindiga sun banka wa gidaje da ƴan gudun hijira wuta, mutane fiye da 200 sun mutu
Mai magana da yawun direbobin NURTW masu tuka manyan motoci, a tashar mota ta Laranto da ke Jos, Mahmud Jafaru, ya yi karin haske kan lamarin.
Mahmud Jafaru ya ce babbar motar tana kan hanyarta ta zuwa birnin Fatakwal, jihar Rivers lokacin da maharan suka farmake ta.
Kakakin kungiyar ya kuma bayyana sunayen direbobin da aka kashe da; Haruna Muhammad da Adamu Ibrahim.
Jafaru ya ce:
"Direbobin sun ɗora gari daga Ayangade zuwa Fatakwal lokacin da ƴan bindigar suka kashe su a cikin rana tsaka. Wannan abu ya yi yawa. Rayukan direbobi 'yan Arewa sun koma kamar ba komai ba."

Source: Original
An nemi gwamnati ta kai wa direbobi dauki
Ya ci gaba da cewa:
"Ana kashe Hausawan mu kamar kiyashi. Muddin kai direba ne daga Arewa, ba ka da kwanciyar hankali har sai ka isa Fatakwal, kuma gwamnati da jami'an tsaro ba sa yin komai a kai."
Jafaru ya yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan da suka dace don magance matsalar, domin sun rasa direbobi da yawa, kuma an kona masu motocin miliyoyin Naira.
Lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta jihar Imo, Henry Okoye, game da lamarin, bai ba da amsa ba.
"Dole gwamnonin Arewa su dauki mataki" Hon. Danja
A zantawarmu da Hon. Balarabe Danja, wanda ke kasuwancin dabbobi a Kudu, ya ce akwai bukatar gwamnonin Arewa sun dauki mataki kan kisan da ake yiwa direbobin yankin a Kudu.
Hon Danja ya ce:
"Idan aka zura idanuwa ana kallo ba tare da an dauki mataki ba, to kisan direbobinmu da ke kai kayanmu Kudu zai ci gaba da karuwa.
"Ni ina ga wannan hakkin gwamnonin Arewa ne. Ya kamata su hadu da na Kudu, su tattauna, su kafa sharadi na diyyar duk wani ran direba da aka kashe a hanyar ma damar ba kungiyar ta'addanci ba ce."
Tsohon mai neman takarar kujerar majalisar jihar Katsina domin wakiltar Danja ya ce su kansuwa da ke bin hanyoyin Kudu, suna yi ne a firgice.
Kisan direbobi: Dattawan Arewa sun magantu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, dattawan Arewa sun bayyana matuƙar takaicinsu kan yawaitar kisan Arewa da ake yi a Kudu.
Rahotanni sun nuna cewa ƙungiyoyin IPOB da ESN sun kashe aƙalla direbobin Arewa 20 waɗanda ke jigilar kaya zuwa yankin.
Amma fa, a cewar ACF, gwamnatin tarayya da jami'an tsaro ba su ɗauki matakan da suka dace don dakile waɗannan kashe-kashen ba, lamarin da ka iya zama babban barazana ga zaman lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

