Sabon Bidiyo kan Natasha Ya Yamutsa Hazo, Sanata Ta Shirya Daukar Mataki

Sabon Bidiyo kan Natasha Ya Yamutsa Hazo, Sanata Ta Shirya Daukar Mataki

  • Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti Uduaghan ta bayyana cewa ana shirya sabuwar manakisa domin bata mata suna
  • Ta ce tana sane da wani sabon bidiyo dake yawo, inda aka ji wata da aka yi zargin ita ce ta fadi wasu kalamai a kan shugaban kasa
  • A martaninta, Natasha Akpoti ta nesanta kanta daga bidiyon da sautin, tana cewa an kirkire su ne da fasaha domin tayar da zaune tsaye

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana a cewa bata da wata alaka da wani faifan sauti da bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Bidiyon da ake magana a kai yana zargin cewa tana magana da wani ɗan jarida, ta kuma ce shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi barazana ga shugaba Bola Tinubu domin a tsare ta.

Kara karanta wannan

Yadda sahar Facebook ta kulla auren so da kauna a Jihar Kano

An fitar da sabon bidiyo kan Natasha
Sanata ta karyata cewa ita ce a wani bidiyo da ya karade kafar sada zumunta Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a cikin wata sanarwa da Natasha ta fitar a Abuja, ta nesanta kanta daga abin da ke cikin bidiyon, tana rokon jama'a da su yi watsi da shi gaba ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Natasha ta musanta magana kan Tinubu

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa Natasha ta bayyana wannan bidiyo da sautin da ke yawo a matsayin ƙarya da aka tsara da gangan domin bata mata suna da kuma haddasa rudani a majalisar dokoki.

Sanarwar ta ce:

"Na nesanta kaina daga wannan bidiyo da sautin da ke yawo. Ban taɓa irin wannan hira ko makamanciyar wannan magana da wani ɗan jarida ko wani mutum ba. Muryar da ke cikin sautin ba tawa bace — an kirkire ta ne kuma an yi amfani da fasaha wajen canza ta domin cin mutuncina."
"Shi wannan abu, yunkuri ne na gangan domin karkatar da hankalin jama'a, bata sunana, da kuma tayar da zaune tsaye a tsakanin shugabannin majalisar dokoki da gwamnatin tarayya."

Kara karanta wannan

'Tun a tafiya motarmu ke samun matsala,' Yar wasan Kano ta fadi 'dalilin' hadarinsu

Sanata Natasha za ta ɗauki matakin shari’a

A ci gaba da bayaninta, Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti Uduaghan ta jaddada cewa za ta ci gaba da tsaya wa bisa gaskiya da adalci.

Ta kuma bayyana cewa ta umarci lauyoyinta tare da hukumomin tsaro da su gudanar da bincike a kan tushen wannan bidiyo da sauti.

Natasha ta ce ana son bata mata suna
Natasha ta zargi wasu mutane da kokarin kawo rudu a majalisa Hoto: Natasha H Akpoti/Godswill Obot Akpabio
Source: Twitter

Ta ce:

"Jama’a su dauki wannan bidiyo da sautin da ke yawo a matsayin ƙarya tsagwaronta kuma cike da yaudara. Wannan aiki ne na wasu mutane marasa kishin kasa da ke ƙoƙarin bata suna na."
"Zan ci gaba da ba da hidima ga jama’a bisa gaskiya da rikon amana. Ina kuma rokon ‘yan Najeriya da su kasance masu wayewa da lura da irin waɗannan ƙetare-da-iyaka na yaɗa ƙarya da amfani da fasaha wajen kwaikwayon mutane domin tayar da hayaniya a siyasa."

An kai hari gidansu Sanata Natasha

A wani labarin, kun ji cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari gidan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke Ihima, karamar hukumar Okehi a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Zargin da ake yi ya tabbata, auren fitacciyar jarumar Nollywood ya mutu

Rahotanni sun bayyana cewa harin ya auku ne da safiyar ranar Litinin, 3 ga Yuni, 2024, inda masu hari suka lalata wasu sassa na gidan, sai dai ba a bayar da rahoton illata kowa ba.

Wani kusa da Sanata Natasha ya tabbatar da lamarin, ya ce maharan sun far wa gidan ne da bindigogi da sauran makamai, suka kuma yi kaca-kaca da wasu kayan cikin gidan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng