Bayan Mutane Sama da 1,595 Sun Mutu, An Ji Dalilin Rushewar Gine Gine a Najeriya
- Masana sun zargi rashin shugabanci nagari a bangaren injiniyanci da zama silar yawaitar rushewar gine-gine a Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa rushewar gine-gine ya kashe mutane 1,595 a Najeriya tun daga 1974 zuwa 2025, mafi akasari a jihar Legas
- Farfesa Okorie Uche ya bukaci a bai wa injiniyoyi iko su jagoranci aikin gini tare da fifita nagarta da aminci fiye da ribar gajeren lokaci
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Masu ruwa da tsaki a bangaren injiniya sun bayyana rashin ingantaccen tsarin gudanar da aikin injiniyanci a matsayin babbar matsala da ke haddasa yawan rushewar gine-gine a Najeriya.
Sun bayyana hakan ne a lokacin babban taron shekara karo na biyar na girmamawa ga Injiniya Umar Jibrin da cibiyar NICE ta shirya a ranar Asabar a birnin Abuja.

Source: Twitter
Taken taron ya kasance: “Ingantaccen gudanar da ayyukan injiniyanci a matsayin maganin rushewar gine-gine”, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
An magantu kan yawan rushewar gine-gine
An shirya taron ne domin girmama Jibrin wanda ya sadaukar da shekaru da dama wajen amfani da ilimin injiniyanci domin ci gaban kasa.
Babban bako mai jawabi, Farfesa Okorie Uche, wanda shi ne magatakardar hukumar kula da ayyukan injiniyanci a Najeriya (COREN), ya ce rushewar gini babbar damuwa ce a kasa.
Ya danganta hakan da rashin masu kulawa da aikin da suka cancanta, amfani da kayan gini marasa inganci, rashin aiwatar da dokoki.
Sauran sun hada da; amfani da tsare-tsaren gini da suka tsufa ko marasa dacewa, cin hanci wajen bayar da izinin gine-gine da kuma rashin kula da gine-gine bayan an kammala.
Tarihin rushewar gine-gine a Najeriya
Kungiyar hana rushewar gine-gine ta bayyana cewa Najeriya ta samu mace-mace 1,595 a cikin rahotannin rushewar gine-gine guda 640 daga watan Oktoba 1974 zuwa 9 ga Janairu, 2025.
Kungiyar ta ce rushewar gini na farko da aka rahoto a Najeriya ya faru ne a watan Oktoba na shekarar 1974 a jihar Oyo, inda wani ginin bene ya rushe tare da hallaka mutane 27.
Ta kara da cewa:
“Jihar Legas ce aka fi samun yawan rushewar gine-gine a Najeriya, inda take da kashi 55.15 cikin 100 na dukkanin rahotannin.
"Abuja na matsayi na biyu da kashi 4.37%, sai Anambra da 4.06%, Oyo 3.44%, da Kano da 3.28%.
"Wasu jihohi kamar Taraba, Bayelsa, Gombe da Yobe sun fara samun irin wannan rahoto a shekarar 2022.
"A daya hannun, jihohin Zamfara, Taraba, Yobe, Bauchi, Bayelsa, Sokoto, Gombe, Katsina da Kebbi sun samu rahoton rushewar gini sau daya kacal.
"Shekara mafi yawan rushewar gine-gine ita ce 2022, inda aka samu rahotanni 62 a fadin kasa, Legas na da 20 daga ciki (kashi 32%).
"A 2023, an samu rushewar gine-gine 52, inda Legas ta dauki 17 daga ciki (kashi 33%). A 2024 kuma, an samu rushewar gine-gine 47 a jihohi 14, Legas na da mafi yawa da 13 daga ciki.”

Source: Twitter
Me ke jawo yawan ruftawar gine-gine?
A zantawarmu da masani kan harkar gine-gine, Arch. Abdullahi Rabiu a Abuja, ya ce ana samun yawaitar rushewar gine-gine saboda wasu dalilai da dama.

Kara karanta wannan
An fara raba tallafin gwamnatin Tinubu, mutane miliyan 15 za su ci gajiyar shirin
Arch. Abdullahi ya ce:
"Ana iya samun kuskuren farko daga wanda ya zana gidan, yana mai cewa kura-kurai a wajen kayyade adadin nauyin da gini zai iya dauka na jawo ruftawarsa."
Mai zane-zanen gidan ya ce idan ba a samu matsala daga zane ba, to ana iya samun matsala daga wadanda za su yi ginin, walau kin bin tsarin zanen, ko amfani da kayan aiki marasa kyau.
"Kiyaye tsarin amfani da siminti, ruwa, yashi, duwatsu ko kuma kin yin amfani da kayan aiki masu kyau na sa gini ya rufta tun kafin ma a kammala shi.
"utane na amfani da wadanda basu kware ba a wajen gini saboda gudun biyan kudi masu yawa, wanda hakan ke jawo rushewar gini da asarar rayuka."
- Abdullahi Rabiu.
Gini mai hawa 3 ya rufta kan mutane
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gini mai hawa uku ya rushe a yankin Ojodu-Berger, Legas, mutane da dama suka makale, wasu kuma aka ceto su da rai.
Ginin da ya rushe na da gidan cin abinci Equal Rights a kasa, yayin da sauran hawaye uku ba su da mazauna a ciki.
A zantawarmu da masani kan harkar gine-gine, Arch. Abdullahi Rabiu a Abuja, ya bayyana abubuwan da ke jawo gini rugujewa.
Asali: Legit.ng


